Masu Garkuwa Da Suka Sace Mutane a Kauyen Abuja Sun Bayyana Kudin Fansa Da Suke Nema a Biya

Masu Garkuwa Da Suka Sace Mutane a Kauyen Abuja Sun Bayyana Kudin Fansa Da Suke Nema a Biya

  • Rahotanni sun bayyana cewa, wadanda suka yi garkuwa da mazauna unguwar Sabo, a birnin tarayya Abuja, sun kira waya, kuma sun bukaci naira miliyan 15
  • Makonni biyu da suka gabata ne masu garkuwa da mutanen suka shiga garin Sabo, inda suka yi awon gaba da wasu mutane biyu
  • Ko da aka tuntubi rundunar 'yan sanda ta babban birnin tarayyar, mai magana da yawun rundunar ta ce suna kan gudanar da bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wadanda suka yi garkuwa da wasu mutane biyu mazauna unguwar Sabo a karamar hukumar Kuje, a babban birnin tarayya Abuja, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 15.

Jaridar 'City and Crime' sun ba da rahoton cewa, makonni biyu da suka gabata, masu garkuwa da mutane sun farmaki yankin Sabo, tare da yin garkuwa da wasu mazauna garin, da aka bayyana sunayen su da Bissalla Yusuf da Mohammed Ibrahim.

Kara karanta wannan

Abin tausayi yayin da direba ya murkushe masu sharan titi 2 a kokarin kauce wa kamun jami'an LASTMA

Rundunar 'yan sanda
Hukumar 'yan sanda ta ce tana bincike kan lamarin, bayan da masu garkuwar su ka bukaci kudin fansa Hoto: Nigerian Police
Asali: Twitter

Wani daga cikin iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “da misalin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, shugaban masu garkuwar ya kira waya, ya bukaci naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar 'yan sanda na gudanar da bincike

Ya kuma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun sace kayan abinci da wasu kayayyakin masarufi a lokacin da suka kai farmakin.

A baya, kun ji cewa ‘yan bindigar da yawansu ya kai mutum biyar sun farmaki wani kauye mai makwabtaka da garin Agwe, inda suka yi awon gaba da kayan abinci, tabarma, da tsabar kudi har naira miliyan 3.2 a makon jiya.

Ko da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, ta bukaci wakilinmu da ya ba ta lokaci domin ta samu jin ta bakin ofishin rundunar na Kuje.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wasu ‘yan bindiga sun bindige shugaban jam’iyyar siyasa a jihar Anambra

An yi garkuwa da mutane da dama a Abuja

Legit Hausa ta ruwaito maku yadda masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da mutum 29, mazaje, matan aure da kananan yara a kauyen Yewuti, garin su tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matan aure biyu, Zainab Umar da Aisha Zubairu, sun samu sun gudo lokacin da ake tafiya da su cikin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel