Tsugune Ba Ta Ƙare Ba Yayin da NNPCL Ta Sake Korafi Kan Bashin 2.8trn Na Cire Tallafi

Tsugune Ba Ta Ƙare Ba Yayin da NNPCL Ta Sake Korafi Kan Bashin 2.8trn Na Cire Tallafi

  • Yayin da kamfanin NNPCL ke ikirarin bin Gwamnatin Tarayya bashin makudan kudi game da cire tallafin mai, za a kaddamar da binciken
  • Gwamnatin ta shirya kaddamar da bincike kan zargin rike kudin kamfanin har N2.8trn na kuɗin tallafin mai wanda NNPCL ke biya
  • Bayan sanar da cire tallafin mai, shugaban NNPCL, Mele Kyari ya fito ya fadi yawan bashin da kamfanin ke bin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya sake yin duba kan bashin N2.8trn na cire tallafin mai a Najeriya.

Gwamnatin za ta yi binciken kan kudin ne da kamfanin man NNPCL ya yi ikirarin binta bashi na cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

"Yana da kyau amma...": Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan harajin CBN

Gwamnati za ta binciki bashin tallafin mai na N2.8trn da NNPCL ta yi ikirari
Kamfanin NNPCL ya yi korafi kan bashin N2.9trn na tallafin mai. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, NNPC Limited.
Asali: Facebook

Nawa kamfanin NNPCL ke bin bashi?

Hukumar bincike ta KPMG ta gudanar da bincike kan kuɗin tun farko inda ta rage zuwa N2.7trn daga N6trn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ya tattaro cewa an sanar da sake binciken ne a ganawar kwamitin rarraba kudin kasa da aka gudanar a watan Maris din wannan shekara.

Kwana daya bayan rantsar da Shugaba Bola Tinubu, shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce kamfanin ya na bin gwamnatin bashin N2.8trn na tallafin man fetur.

Kyari ya ce tun bayan samar da N6trn a 2022 da kuma N3.7trn a 2023, ba su samu ko da sisin kwabo ba daga Gwamnatin Tarayya, cewar Vanguard.

Kudin da aka biya NNPCL na tallafi

"Tun bayan biyan N6trn a 2022 da kuma N3.7trn a 2023, gwamnati ba ta sake biyan ko da sisin kwabo ba."

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya ta nemi cin hancin $150m daga Binance? Gaskiya ta fito

"Wannan shi ke nuna gwamnatin ta gaza biyan kudin wanda mune muke biya daga asusun kamfani domin ba da gudunmawa kan kudin tallafi."
"Muna jiransu su biya bashin N2.7trn na kudin tallafi, ba zamu iya ci gaba da biyan kudin ba."

- Mele Kyari

Ministan kudi, Wale Edun yayin martaninsa ya ce Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da bincike kan ikirarin gaza biyan N2.7trn.

NNPCL zai dauki matakin kan wahalar mai

Kun ji cewa kamfanin mai na NNPCL ya haɗa kai da jami'an tsaro domin dakile masu boye mai saboda wasu dalilai.

Wannan matakin na NNPCL na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsada da kuma wahalar mai a faɗin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel