Labarai daga jaridun Najeriya a yau

Labarai daga jaridun Najeriya a yau

labarai daga jaridun Najeriya a yau Alhamis 28 ga watan Yuli

Labarai daga jaridun Najeriya a yau

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, yan sanda sun kama wani mai siyar da kayan tebur a wata kasuwa dake 23 Road, FESTAC a jihar Lagasa, mai suna Ikechukwu Alu sakamakon fyade da yayi wa wata yarinya yar shekara 7 mai suna Victoria.

An bayyana cewa an aiki yarinyar siyar katin waya, inda ta batar a hanyan ta na komawa gida, bayan ta koma gida aka korata neman katin, a nan ne Ikechukwu ya dauketa yaje yayi mata fyade.

Jaridar The Nation ta ruwaito inda, hukumar Department of State Services (DSS), na jihar Kogi ta kama wasu da ake zargin masu satar mutane 10 a cikin makkoni shidda a jihar.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta bada umarnin kama shugaban APC

Daraktan jami’an na jihar, Mr Joseph Okpo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanya hannu ya kuma bai wa jaridar News Agency of Nigeria (NAN) a ranar Alhamis a babban birnin Tarayya Abuja.

A cikin Jaridar Daily Independent mun ji cewa, Chief Audu Ogbeh, Ministan aikin gona da raya karkara, yace ma’aikatar noma zata fara shuka ciyawa na musamman saboda shanaye a watan Augusta.

Ogeh ya bayyana haka ne a gurin wani zantawa tare da manema labarai a ranar Laraba a Abuja, yace ma’aikatar ta fara shigo da ciyawan na mussaman cikin kasar. Ya kuma bayyana cewa wannan zai kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

Daga karshe jaridar The Sun ta ruwaito cewa,Tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ceto tattalin arzikin kasa daga barin afkawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel