'Yan Bindiga Sun Ƙara Shiga Abuja, Sun Tafka Ɓarna Yayin Da Suka Yi Garkuwa Da Mutane

'Yan Bindiga Sun Ƙara Shiga Abuja, Sun Tafka Ɓarna Yayin Da Suka Yi Garkuwa Da Mutane

  • Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan uwan juna biyu da wani mai gidan ruwan leda a yankin Bwari da ke birnin tarayya Abuja
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kira dangin wadda suka sace, sun nemi kuɗin fansa
  • Shugaban ƙauyen da lamarin ya afku ya tabbatar inda ya ce wannan ne karo na farko da irin haka ya faru a garin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan uwa biyu a ƙauyen Bmuko da ke kan hanyar Dutse zuwa Bwari a karamar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.

Yan bindiga sun kara kai hari Abuja.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Juna Biyu da Mai gidan Ruwa a Abuja Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta fahimci cewa kwanan nan wasu miyagu suka sace mai gidan ruwan leda daga cikin gidansa a yankin Garejin manyan motoci duk a Bmuko.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro, ƙungiyoyin ƙwadago NLC da TUC sun kira babban taron NEC kan wasu batutuwa

Garin Bmuko na tattare da wuraren haƙar ma'adanai da dama da kuma manyan motocin da ke jigilar duwatsu zuwa wasu sassan babban birnin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake hira da ƴan jarida ranar Jumu'a da ta gabata, mai gidan hayar da ƴan uwan da aka sace ke zaune, Michael Uwaipo Sylva, ya ce:

"Da farko sun shiga gidan maƙoci amma suka taras baya nan, daga bisani suka shiga gidan da ƴan uwan ke zaune, suka yi awom gaba da su."
"Namijin cikinsu ya samu nasarar guduwa daga hannun ƴan bindigan a hanyar zuwa cikin daji amma ita ƴar uwarsa mace sun tafi da ita."

Shin an nemi kuɗin fansa bayan faruwar lamarin?

Mista Sylva ya ƙara da cewa ya samu labarin maharan sun kira ƴan uwan wacce suka yi garkuwa da ita kuma sun nemi a harhaɗa musu kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Miyagu sun kai kazamin hari gidan babban jigon PDP kuma tsohon kwamishina, sun jefa bama-bamai

"Masu garkuwan sun tuntuɓi danginta yanzu haka sun nemi a biya Naira miliyan ɗaya a matsayin kuɗin fansa."

Shugaban Bmuko, Ibrahim Y Dangana, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana shi a matsayin irinsa na farko a yankin, PM News ta ruwaito.

"Kwanakin Ƴan Ta'adda Sun Kusa Ƙarewa"

A wani rahoton na daban Hedkwatar tsaro DHQ ta yi iƙirarin cewa ragowar kwanakin da suka rage wa ƴan ta'adda a duniya ba su da yawa kuma a kididdige suke.

Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya ce sojoji sun tura yan bindiga 67 barzahu sun kama 170 a makon jiya kaɗai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel