Rayukan Mutum 3 Sun Salwanta a Wani Kazamin Hatsarin Mota a Jihar Legas

Rayukan Mutum 3 Sun Salwanta a Wani Kazamin Hatsarin Mota a Jihar Legas

  • Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu ababen hawa biyu a kan titin hanyar Itamaga zuwa Ijede a jihar Legas
  • Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum uku ciki har da ɗalibai biyu da raunata wasu mutum biyu
  • Hatsarin dai ya auku ne a sakamakon tsananin gudu da direban wata motar ƙirar Toyota Camry wacce ta afka kan wata Keke Napep

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Legas - Mutum uku sun mutu a ranar Talata yayin da wasu mutum biyu suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Itamaga zuwa Ijede a garin Ikorodu na jihar Legas.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa hatsarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 8:05 na safe, ya haɗa da wata mota ƙirar Toyota Camry da wata Keke Napep.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka mutum 1 da sace wasu mutum 25 a wani sabon hari a Kaduna

Mutum uku sun mutu a wani hatsarin mota a Legas
Wani hatsarin mota (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: pmnews.com
Asali: UGC

Motar wacce ke sharara gudu, an ce ta tsallaka ɗayan gefen titin ne inda ta afka kan Keke Napep ɗin, wanda nan take ta kashe fasinjoji uku, babban mutum ɗaya da kuma yara ƴan makaranta guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaya daga cikin wadanda suka jikkata, wani ɗalibin makarantar sakandare, wanda ya sume, an garzaya da shi asibiti tare da direban Keke Napep ɗin domin duba lafiyarsu.

Sai dai, direban motar Camry ɗin ya ranta a na kare bayan aukuwar hatsarin.

Yadda hatsarin motar ya auku

Wani shaidar ganau ba jiyau ba a wajen da hatsarin ya auku, ya ce motar ta taho ne zuwa Ijede, wani ƙauye a Ikorodu, kuma tana sharara gudu wanda hakan ya sanya ta ƙwace wa diraban, kafin ta afka kan Keke Napep ɗin wacce ke tafiya zuwa garejin Ikorodu.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Hatsarin motar ya auku ne a kusa da tashar mota ta Cele a ƙauyen na Ijede, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga baya, jami'an ƴan sanda sun zo wurin da hatsarin ya auku inda suka ɗauki ababen hawan da hatsarin ya ritsa da su zuwa ofishin ƴan sanda da ke Ijede.

Fasinjoji 18 Sun Tsallake Rijiya da Baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla fasinjoji 18 suka tsallake rijya da baya a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su a jihar Legas.

Fasinjojin dai suna cikin wata motar bas ƙirar Mazda wacce ke tafiya kan titin hanyar Legas zuwa Ibadan lokacin da hatsarin ya auku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng