Wike Ya Dakata, Ya Hakura da Maganar Karbe Filayen Masallatai da Coci a Abuja

Wike Ya Dakata, Ya Hakura da Maganar Karbe Filayen Masallatai da Coci a Abuja

  • Nyesom Wike ya zauna da shugabannin majalisar babban masallacin Abuja a karkashin jagorancin Alhaji Yahaya Abubakar
  • Mai martaba Etsu Nupe ya ba Ministan uzuri a kan abin da ya hana su karasa gina wasu filayen da su mallaka a birnin Abuja
  • Wike ya yi la’akari da dalilan da aka bada, ya tsawaita wa’adin watanni uku da ya bada domin karbe filayen da aka yi watsi da su

Abuja - Ministan harkar Birnin Tarayya na Abuja, Nyesom Wike, ya tsawaita wa’din da ya ba wadanda su ka mallaki filaye a garin Abuja.

Kafin yanzu, Vanguard ta ce Mai girma Ministan ya bada umarni ga duk mai fili ya yi kokarin gina shi ko kuwa gwamnatinsa ta karbe.

Da ya yi zama da shugaban majalisar kula da babban masallacin Abuja, Alhaji Yahaya Abubakar, Nyesom Wike ya tsawaita wa’adin.

Kara karanta wannan

Wayyo ‘Yan Bindiga Za Su Karasa Mu – ‘Dan Majalisa Ya Kai Kuka Wajen Gwamnati

Nyesom Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Nyesom Wike ya janye wa'adinsa a Abuja

A maimakon watanni uku da Wike ya bada da farko, alfarmar Mai martaba Etsu Nupe ta sa gwamnati ta yi wa masallacin rangwame.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lura da cewa kungiyoyin addini sun dogara ne da gudumuwar al’umma, ministan Abujan ya yarda ya dakata da maganar karbe fulotin.

Tawagar Mai martaba Yahaya Abubakar ta je hukumar FCTA ne domin neman karin haske a game da wani filin ta da aka ce ta tsaida gini.

Uzurin da aka ba Ministan birnin Abuja

Sarkin ya fadi dalilin dakatar da aikin da su ka dauko, ya ce hukuma ta umarce su tsaida ginin da su ke yi daura da cibiyar Shehu Yar’Adua.

Rahoton ya ce Etsu Nupe ya yi amfani da damar wajen neman alfarmar FCDA domin karasa mata gyaran babban masallacin da aka fara.

Kara karanta wannan

Ba Na Adawa Da Addinin Musulunci a Matsayina Na Ministan Abuja, Wike

Hukumar FCDA ta dauki nauyin gyare-gyaren kafin Bola Tinubu ya karbi mulki a Mayu.

A game da wani filinsu da ya jawo abin magana, Sarkin ya ce sun samu izini kuma ba da dadewa ba za a fara ginin kamar yadda ya dace.

A game da zargin ya rusa masallaci da ya ke gwamna a Ribas, Nyesom Wike ya ce sharrin ‘yan adawa ne, bai rusa wurin ibada a mulkinsa.

An kai wa gwamnati kuka

An rahoto Hon. Yusuf Kure Baraje ya na cewa an kai hare-hare fiye da 10 a kauyensa a jihar Neja, ya ce ‘yan bindiga sun je har gidansa.

Baraje yake cewa bai taba ganin sojoji sun fito za su yaki ‘yan bindiga ba duk ya na ikirarin jami’an tsaron sun san inda miyagun su ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel