Bayan Ganawa Da Kungiyar Dalibai Ta NANS, Jami’ar Legas Ta Rage Kudin Makaranta

Bayan Ganawa Da Kungiyar Dalibai Ta NANS, Jami’ar Legas Ta Rage Kudin Makaranta

  • Yayin da ake zanga-zanga a jami’o’in Najeriya, wasu sun fara jin korafin dalibai a kasar
  • Jami’ar Legas wanda ta fuskanci zanga-zanga a ranar Laraba, ta rage kudin makaranta a yau
  • Wannan na zuwa ne bayan kungiyar dalibai ta NANS ta yi wata ganawa da hukumar makarantar

Jihar Legas – Bayan ganawar da Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS) da yi da jami’ar Legas, hukumar makarantar ta rage kudin makaranta.

Hukumar makarantar karkashin jagorancin Farfesa Folasade Ogunsola ta gana da kungiyar daliban a ranar Alhamis 14 ga watan Satumba.

Jami'ar Legas ta rage kudin makaranta
Jami’ar Legas Ta Rage Kudin Makaranta Bayan Ganawa Da NANS. Hoto: Jami'ar Legas.

Meye dalilin rage kudin a jami'ar Legas?

Daliban wanda shugabansu, Usman Barambu ya jagoranta ya yi ganawa da hukumar makarantar kan wannan karin kudi na dalibai, Premium Times ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kashe-Kashe: Matar Tinubu Ta Raba N500m a Arewacin Najeriya, Babu Musulmi 1 da Ya Samu

Jami’ar Legas ta kara kudin makaranta daga Naira dubu 26 da dubu 76 zuwa Naira dubu 120 da kuma Naira dubu 240, ya danganta da tsangayar da dalibi ya ke.

Kakakin jami’ar, Adejoke Alaga-Ibrahim ya tabbatar da rage kudin makarantar a yau Juma’a 15 ga watan Satumba, Legit ta tattaro.

Yaushe aka sanar da rage kudin a jami'ar Legas?

A cikin sanarwar, an rage kudin makarantar daga dubu 126,325 zuwa dubu 116,325 ga tsangayoyin da ba sa shiga dakunan gwaje-gwaje.

Har ila yau, tsangayoyi ma su shiga dakin gwaje-gwaje, an rage kudin daga dubu 176,325 zuwa dubu 166,325.

Har ila yau, an rage kudin sabbin dalibai daga Naira dubu 126,325 zuwa 116,325 wadanda ba sa shiga dakin gwaji.

An kuma ragewa dalibai masu amfani da dakunan gwaji daga dubu 176,325 zuwa 166,325.

Yayin da tsoffin dalibai wadanda ba sa shiga dakin gwaji aka rage daga dubu 100,750 zuwa 80,750.

Kara karanta wannan

Mai Dakin Tinubu Ta Yi Kyautar Ban Mamaki, Ta Rabawa Mutane N500m a Filato

Wadanda ke amfani da dakuna gwaji kuma an rage daga dubu 140,250 zuwa 120,250 sai kuma daga dubu 190,250 zuwa 170,250 ga daliban da ke bangaren lafiya.

Daliban Jami'ar Jos sun yi zanga-zanga kan kudin makaranta

A wani labarin, daliban Jami'ar Jos sun yi dafifi a kan tituna inda su ke zanga-zangar karin kudin makaranta a Jami'ar.

Daliban sun bayyana cewa halin da su ke ciki na matsin tattalin arziki kadai ta ishe su, amma za a kara musu kudin makaranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel