Borno: Jirgin Sojin Sama Ya Ragargaji Yan Ta'adda da Yawa a Yankin Tafkin Chadi

Borno: Jirgin Sojin Sama Ya Ragargaji Yan Ta'adda da Yawa a Yankin Tafkin Chadi

  • Jirgin NAF ya halaka gomman mayaƙan ƙungiyoyin 'yan ta'adda yayin da ya kai samamen ruwan wuta ta sama a Tafkin Chadi
  • kakakim NAF na ƙasa ya bayyana cewa luguden wutan ya yi fata-fata da maɓoyar yan ta'addan tare da lalata kayan aikinsu
  • Ya jaddada cewa yunkurin hukumar soji na kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a Arewa maso Gabas na nan daram

Jihar Borno - Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa jirgin yaƙinta ya samu nasarar halaka gomman mayakan Boko Haram da ISWAP a yankin Tafkin Chadi a jihar Borno.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar sojojin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Jirgin yakin rundunar NAF.
Borno: Jirgin Sojin Sama Ya Ragargaji Yan Ta'adda da Yawa a Yankin Tafkin Chadi Hoto: NAF
Asali: UGC

Ya bayyana cewa ruwan bama-baman jirgin yaƙin ya yi fata-fata da maɓoyar 'yan ta'addan, kana ya lalata tsarukansu da kayan aikinsu da ke yankin tafkin Chadi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hatsabibin Dan Ta'addan Da Ke Yawan Kashe Jama'a Ya Gamu da Ajalinsa a Jihar Arewa

Ya ce sojojin saman sun kai wannan samamen ne a tsakanin 27 zuwa 30 ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar 'yan ta'addan a Tumbun Fulani da Tumbun Shitu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa bayanan 'yan leƙen asiri ya nuna cewa 'yan ta'addan na kulle-kullen yadda zasu ƙaddamar da hari kan sojoji da fararen hula, Punch ta tattaro a rahoto.

A garin Tumbun Fulani, an ga ‘yan ta’adda na loda jarkoki a cikin manyan motoci guda biyu da aka boye a karkashin bishiyoyi.

Daga bisani, jirgin NAF ya tashi domin lalata wurin, wanda aka yi imanin cewa babban tushe ne na kayan aikin 'yan ta'addan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Yadda jirgin ya saki ruwan wuta kan 'yan ta'addan

A cewar kakakin NAF, bayan tabbatar da bayanin abinda ke wakana a wurin, jirgin ya saki ruwan bama-bamai, wanda daga bisani aka gano cewa mayaƙa da yawa sun mutu kuma an lalata motocinsu na yaƙi.

Kara karanta wannan

Karin Albashin N35k Da Jerin Tallafin Da Shugaba Tinubu Ya Fito Da Su Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Ya ce an kuma kai hare-hare makamancin haka a Tumbun Shitu bayan an ga wasu gine-ginen da ake kyautata zaton maboyar ‘yan ta’adda ne a boye a cikin wuri mai duhu.

Ya ce bayanan da aka tattara kan harin da aka kai ta sama ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata manyan motocinsu.

“Kudirin da rundunar sojojin Najeriya ta yi na takaita ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas da ma sauran sassan Najeriya na nan daram." in ji shi.

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Harin Ta'addanci a Jihar Sokoto, Sun Kashe Rayuka

A wani rahoton kuma Wasu 'yan sa'kai sun fusata sun kai harin ɗaukar fansa rugar Fulani jim kaɗan bayan wasu mahara sun kashe jama'a a kauyen Soro.

Rahoto ya nuna yan bindigan da ake zargin Fulani ne sun kashe mutane uku kana suka yi awon gaba da wasu da dama a jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Jami'ar Jihar Chicago: Peter Obi Ya Taso Tinubu a Gaba Kan Takardun Bayanan Karatunsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel