Bidiyon Ministan Abuja Wike Yana Girki Yayin da Gbajabiamila Ke Kallo Ya Yadu

Bidiyon Ministan Abuja Wike Yana Girki Yayin da Gbajabiamila Ke Kallo Ya Yadu

  • Sunan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sake hawa kanen labarai saboda wani bajinta da ya nuna
  • An dauki bidiyon tsohon gwamnan na jihar Ribas yana girka abinci a kicin yayin da yake tare da abokansa a ranar hutu
  • An gano Wike yana juya miya a cikin tukunya yayin da shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya tsaya yana kallo

Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya nunawa yan Najeriya cewa shi mutum ne da ya kware a bangarori daban-daban.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, an gano tsohon gwamnan na jihar Ribas a cikin kicin yana baje kolin kwarewarsa a harkar girke-girke inda aka gano shi yana juya tukunyar miya.

Wike ya zage damtse yana girki
Bidiyon Ministan Abuja Wike Yana Girki Yayin da Gbajabiamila Ke Kallo Ya Yadu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/Femi Gbajabiamila
Asali: Facebook

An kuma gano tsohon kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila a cikin kicin din yana kallon yadda Wike yake girki.

Kara karanta wannan

“Ina Girmama Kudi”: Kyakkyawar Budurwa Ta Auri Dattijo, Ta Nunawa Duniya Shi a Bidiyo

Wike ya shiga sahun mutane kamar su Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, wanda shima aka dauke shi a bidiyo yana baje kolin kwarewarsa a bangaren girki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a sun yi martani kan bidiyon Wike yana girki

A halin da ake ciki, yan Najeriya sun yi martani a kan bidiyon Wike yana girki tare da abokinsa Gbajabiamila a kicin.

A cikin da gajeren bidiyon, Mista Thomas Shelby OBE ya bayyana Wike a matsayin mutumin da ke da fasaha iri-iri.

Ya rubuta a shafinsa na X, @ChroniclesPHC:

"WIKE mutum ne mai fasaha iri-iri...."

@pretoriadaddyPya ce:

"Kalli tsohon gwamna na ya zama mai girki."

@ibadanguy ya ce:

"Hatta gbajabiamila bai manta cewa wike ne ke girki ba sai da ya tsaya kusa da shi a yayin da yake girki dole namiji ya tsaya kusa da shi yayin girkin duk da cewar ba komai yake yi ba."

Kara karanta wannan

Zuwan Wike Abuja: Jigon APC ya fadi babban abin da Wike zai yi a matsayin minista

@muels_SK ya ce:

"Mai gidan Abuja kan aiki."

"Litar Man Fetur Zata Karye Ta Dawo N180 a Najeriya" Fitaccen Malami Ya Fadi Lokaci

A wani labarin, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa farashin man fetur zai fadi warwas daga N617 kan kowace lita a yanzu zuwa N180.

Ayodele wanda ya yi hasashen a cikin wani sabon bidiyo ya bukaci yan Najeriya da su sa rai da hakan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel