“Ba Haushi Na Zo Yi Maku Ba”: Soyinka Ya Caccaki Obasanjo Kan Harin Sarakunan Yarbawa

“Ba Haushi Na Zo Yi Maku Ba”: Soyinka Ya Caccaki Obasanjo Kan Harin Sarakunan Yarbawa

  • Shahararren marubuci, Farfesa Wole Soyinka, ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wankin babban bargo kan muzanta sarakunan Yarbawa
  • An gano Soyinka yana jawabi ga sarakuna cewa bai halarci taron don yi masu haushi cewa su tashi ko su zauna ba, wani abu da Obasanjo ya aikata kwanan nan
  • Wasu yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na bidiyon, cewa fadan Obasanjo da Soyinka ba zai taba karewa ba

Abeokuta, Ogun - An hasko Wole Soyinka, shahararren marubuci a Afrika, yana shagube ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo.

A kwanan nan ne Obasanjo ya sha suka saboda cin zarafin da ya yi wa sarakunan gargajiya a jihar Oyo, lokacin da ya bukaci su tashi tsaye sannan su zauna saboda sun ki tashi su gaishe shi a lokacin da ya halarci taron kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

Kara karanta wannan

Obasanjo Mugu Ne, Amma Na Yi Maganinsa, Tsohuwar Matar Tsohon Shugaban Kasa Ya Kunto Kura

Soyinka ya yi wa Obasanjo wankin soso da sabulu
“Ba Haushi Na Zo Yi Maku Ba”: Soyinka Ya Caccaki Obasanjo Kan Harin Sarakunan Yarbawa Hoto: Olusegun Obasanjo
Asali: Twitter

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya gayyaci Obasanjo domin ya kaddamar da wani aiki a yankin Iseyin na jihar, amma tsohon shugaban kasar ya kaskantar da sarakunan gargajiya, inda ya bukaci su tashi sannan su auna saboda sun gaishe shi.

Soyinka ya yi martani ga abun da Obasanjo ya yi wa sarakunan gargajiya

A cikin bidiyon wanda Ayekooto ya wallafa a dandalin X, an gano Soyinka yana martani ga abun da tsohon shugaban kasar ya yi lokacin da ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ya masu martabarmu, Ina so na baku tabbacin cewa bana shirin yi maku haushi kan ku tashi sannan ku zauna."

Wasu yan Najeriya sun garzaya sashin kwamet na bidiyon don bayyana ra'ayinsu.

Oghomwen Eregie ya ce adawar da ke tsakanin Soyinka da Obasanjo ba abu ne da zai taba karewa ba.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Matar Obasanjo Ta Dau Zafi, Ta Yi Masa Wankin Babban Bargo

Asade Toba ta bayyana cewa Soyinka ya san yadda ake shagube ga mutum.

Arakunrin Debo ya yi al'ajabin ko gabar da ke tsakanin Obasanjo da Soyinka zai taba karewa.

"Wa zai kawo karshen fadan da ke tsakanin Soyinka da OBJ?"

Abolore Bello ya jaddada cewar mutunta sarakuna na da matukar muhimmanci a al'adar Yarbawa.

"A toh....a matsayin Bayarame muna mutunta sarakunanmu a kodayaushe."

Ga bidiyon a kasa:

Obasanjo ya taba yi min sujjada don na nuna zan bar gidansa, Inji tsohuwar matarsa

A wani labarin, mun ji cewa matar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Taiwo, ta bayyana cewa tsohon shugaban na Najeriya mugun miji ne a lokacin take zaman aure dashi, inda ta ce ya ma taba kuka lokacin da ta bar shi.

Taiwo ya bayyana hakan ne a lokacin da take martani kan maganar da aka yi a kwanan baya na cewa ta kamu da tabin hankal bisa rasa damar ci gaba da zama a gidan Obasanjo, kuma ba matarsa b ace a yanzu duk da haifa masa ‘ya’ya biyu, inji rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel