Obasanjo Ya Taba Yi Min Sujjada Don Na Nuna Zan Bar Gidansa, In Ji Tsohuwar Matarsa

Obasanjo Ya Taba Yi Min Sujjada Don Na Nuna Zan Bar Gidansa, In Ji Tsohuwar Matarsa

  • Taiwo, matar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta ce tsohon shugaban na Najeriya mugun miji ne a lokacin da suke tare
  • A cewarta, Obasanjo ya taba yi durkusawa a gabanta a dakin kwananta ya kuma zubar da kwalla a lokacin da ta bar shi
  • Matar da ta Haifa masa ‘ya’ya biyu, ta ce Obasanjo ne kadai tsohon shugaban da ke caccakar dukkan shugabanin kasar, inda ta ce masa ya yi koyi da sauran shugabannin kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abeokuta, Ogun Matar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Taiwo, ta bayyana cewa tsohon shugaban na Najeriya mugun miji ne a lokacin take zaman aure dashi, inda ta ce ya ma taba kuka lokacin da ta bar shi.

Taiwo ya bayyana hakan ne a lokacin da take martani kan maganar da aka yi a kwanan baya na cewa ta kamu da tabin hankal bisa rasa damar ci gaba da zama a gidan Obasanjo, kuma ba matarsa b ace a yanzu duk da haifa masa ‘ya’ya biyu, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

“Ban Zo Nan Don Na Yi Maku Haushi Ba”: Soyinka Ya Yi Wa Obasanjo Wankin Babban Bargo Kan Sarakunan Yarbawa

Tsoffin ma’auratan dai suna ta zage-zagen juna ne bayan da Taiwo ta nemi afuwar sarakunan Oyo kan kalaman da tsohon shugaban kasar ya yi na cewa ba sa girmama shi.

Yadda tsohuwar matar Obasanjo ta tona asirinsa
Obasanjo mugu ne, inji matarsa | Hoto: @Ohis_Ogwogho
Asali: Twitter

Me yasa uwargidan Obasanjo ke sukar tsohon shugaban kasar?

An ruwaito yadda Obasanjo ya sami sabani da sarakunan gargajiyar Yarbawa kan yadda ya nemi su tashi tsaye su gaishe shi a matsayinsa na uban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda abin ya faru kuwa shi ne, gwamna Seyi Makinde ne ya gayyaci tsohon shugaban kasar ya kaddamar da wani aiki a yankin Iseyin na jihar inda ya gamu da sarakunan a can.

Rahotanni sun ce Obasanjo ya yi gatsali ga sarakunan gargajiyar inda ya ce sun ki tashi su gaishe shi duk da sanin girmansa.

Daga nan ne sai matar ta nemi afuwa a madadin Obasanjo biyo bayan takaddamar da ta auku a tsakaninsu duk da sanin girman juna.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Matar Obasanjo Ta Dau Zafi, Ta Yi Masa Wankin Babban Bargo

Ban hadu da Tinubu ba, inji Obasanjo

A wani labarin, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya musanta ikirarin cewa ya gana da Shugaba Bola Tinubu.

Shugaba Tinubu da Obasanjo alaka ta yi tsami a tsakaninsu tun bayan tsayawansa takara da tikitin Musulmi da Musulmi a 2022.

Obasanjo ya fito karara ya goyi bayan Peter Obi (Labour Party, LP) a lokacin zaben shugaban kasa na 2023, kuma ya rika sukar jam’iyyar APC mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel