Amurka Ta Gargadi Yan Kasarta Kan Zuwa Wasu Jihohin Najeriya

Amurka Ta Gargadi Yan Kasarta Kan Zuwa Wasu Jihohin Najeriya

 • Kasar Amurka ta sake fitar da shawarwari na gargadi game da rashin tsaro a wasu yankunan Najeriya
 • Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta gargadi yan kasarta a kan zuwa wasu jihohi guda 17
 • Ta bayar da shawarwarin ne saboda dalilai na rashin tsaro kama daga ta'addanci, rashin zaman lafiya, garkuwa da mutane da sauransu

Gwamnatin Amurka ta gargadi al'ummar kasar da su kaucewa zuwa wasu yankunan Najeriya saboda laifukan da suka shafi ayyukan ta’addanci, tashe tashen hankula da garkuwa da mutane.

Gwamnatin Amurka ta gargadi yan Najeriya kan zuwa wasu jihohin Najeriya
Amurka Ta Gargadi Yan Kasarta Kan Zuwa Wasu Jihohin Najeriya Hoto: Joe Biden, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Amurka ta yi gargadin ne a cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar kan shawarwarin tafiye-tafiye.

A cikin sanarwar, Amurka ta bukaci yan kasarta da su guji wasu jihohi a yankin arewa, kudu maso gabas da kudu maso kudu saboda laifuka, ta'addanci, rashin zaman lafiya, garkuwa da mutane da sauransu, rahoton Business Day.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

Hukumar ta kuma bayyana cewa laifuka irinsu fashi da makami, cin zarafi, kwace motoci, garkuwa da mutane da fyade sun zama ruwan dare a fadin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan ta'adda na iya kai hare-hare a Najeriya, Amurka ta yi gargadi

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kuma bayyana cewa yan ta'adda na iya kai hare-hare a wurare kamar shagunan siye-siye, kasuwanni, otel-otel, wuraren bauta, gidajen cin abinci, mashaya, makarantu, wuraren gwamnati da sauran wuraren da jama'a ke taruwa.

Sai dai kuma, ta shawarci yan kasarta da ya zama dole su shiga Najeriya a kan su kasance dauke da katin shaidarsu da suka hada da fasfot da bizar Najeriya.

Ta kuma bukaci da su yi taka-tsan-tsan yayin tuki da daddare, su boye kansu; su duba hanyoyin da za su bi sannan kada su yi yunkurin nuna turjiya da jikinsu a yayin yunkurin fashi; da kuma taka-tsan-tsan yayin ziyartan bankuna da ATM.

Kara karanta wannan

Hukuncin Zabe: Hankula Sun Tashi Yayin Da Aka Rufe Shaguna A Kano, Bayanai Sun Fito

Jerin jihohin da Amurka ta bada shawarar matafiya su kaurace musu

 1. Borno
 2. Yobe
 3. Kogi
 4. Adamawa
 5. Gombe
 6. Kaduna
 7. Kano
 8. Katsina
 9. Sokoto
 10. Zamfara
 11. Abia
 12. Anambra
 13. Bayelsa
 14. Delta
 15. Enugu
 16. Imo
 17. Rivers

Tinubu ya sha alwashin yakar talauci da gyara kasar ko da za a tsane shi

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce ko da zai yi bakin jini a idon 'yan Najeriya zai yi kokari wurin gyara kasar.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres a birnin New York na Amurka, TheCable ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel