Tinubu Ya Sha Alwashin Yakar Talauci Da Gyara Kasar Ko Da Za A Tsane Shi A Najeriya

Tinubu Ya Sha Alwashin Yakar Talauci Da Gyara Kasar Ko Da Za A Tsane Shi A Najeriya

  • Shugaba Tinubu ya ce ya dauki alkawarin gyara kasar nan ko da kuwa zai zama mai bakin jini a Najeriya
  • Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres a New York
  • Ya ce shi ma tushensa talauci ne don haka ya kudiri aniyar yakarta don 'yan Najeriya su samu saukin rayuwa

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce ko da zai yi bakin jini a idon 'yan Najeriya zai yi kokari wurin gyara kasar.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres a birnin New York na Amurka, TheCable ta tattaro.

Tinubu ya sha alwashin gyara kasa ko da zai yi bakin jini
Tinubu Ya Sha Alwashin Yakar Talauci Da Gyara Najeriya. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya ce kan gyara Najeriya?

Wannan sanarwar an fitar da ita ne ta bakin kakakinsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale a jiya Alhamis 21 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Roki 'Yan Najeriya Da Ke Amurka Abu Daya Tak, Ya Ce An Samu Sauyin Gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya ce ya himmatu wurin gyara kasar duk da samun tasgaro a baya amma hakan ba zai kashe masa gwiwa ba.

Ya ce:

"Na yi fada don samar da dimukradiyya, an tsare ni a kai, ni yanzu shugaban kasa ne, zan yi kokari don tabbatar da ta tsaya da kafafunta a Najeriya da Afirka.

Tinubu ya ce gwamnatoci sun dage da surutu ba tare da daukar mataki ba na dakile tsananin talauci a kasa, Thisday ta tattaro.

Wane tsare-tsare Tinubu ya shirya na gyara Najeriya?

Ya ce ya himmatu wurin daukar wasu matakai da za su kawo sauyi a irin halin da ake ciki.

Ya kara da cewa:

"Idan aka duba dukkan tushenmu da mu ke nan, duk mu na da alaka da talauci.
"Bai kamata mu ji kunyan tarihinmu ba, ba abun so ba ne, amma ina daya daga cikin wadanda su ka tsira daga kuncin talauci.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Cilla Amurka Don Halartar Muhimmin Taro, An Bayyana Alfanun Taron Ga Najeriya

"Ba zan gajiya ba, sai na kawo sauye-sauye da tsare-tsare da za su sauya Najeriya ko da kuwa za a tsaneni a kasar."

Tinubu ya roki 'yan Najeriya da ke Amurka su dawo gida

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya roki 'yan Najeriya da ke Amurka da su dawo gida inda ya ce yanzu kasar ta sauya.

Tinubu ya fadi haka ne yayin da ya ke ganawa da 'yan Najeriya a birnin New York na Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel