Yau Ake Bikin Yarbawan da Mata Ba Su Fita Waje a Al'adar Jihar Legas

Yau Ake Bikin Yarbawan da Mata Ba Su Fita Waje a Al'adar Jihar Legas

  • A yau Laraba, 16 ga watan Mayu ne ake gudanar da babban bikin al'adar Oro a kasashen Yarabawa da ke Najeriya
  • A bisa al'ada, duk ranar da ake bikin mata ba su fitowa waje sai maza ne za su rika zaga gari ciki kaya na musamman
  • A yankin Ikorodu na jihar Legas, masarautar Ayangburen ta aike ga wani asibiti da buƙatar ma'aikatansu su girmama al'adar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - A yau Alhamis, 16 ga watan Mayu ne za a gudanar da bikin al'adar da mata ba su fita waje a jihar Legas.

ORo fest
Masarauta ta bukaci mata su zauna a gida saboda bikin garajiya a Legas. Hoto: Maxb Network TV
Asali: Facebook

An saba yin bikin al'adar 'Oro' ne a yankin Ikorodu da ke jihar Legas bisa shekara-shekara.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Jaridar Punch ta ruwaito cewa masarautar Ayangburen ce ta sanar da yadda bikin zai gudana a wannar shekarar a cikin wata wasika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masarautar Yarbawa ta rubuta takarda ga asibiti

Mai sarautar gargaya a yankin, Oba Kabiru Shotobi ne ya saka hannu a wasikar tare da aike ta ga ma'aikatan asibiti da suke yankin.

A bisa al'ada, duk ranar da za a gudanar da bikin Oro, mata ba su fita ko da kofar gida ne, rahoton Tribune.

Saboda haka wasikar take dauke da tunatarwa ga matan kan cewa su lizimci gidajensu.

Ga abin da takardar ke cewa:

"A bisa al'ada, a duk lokacin da ake bikin Ore, ana kira ga mata su zauna a ciki gidajensu."
"Saboda haka, muna tunatar ma'aikatan asibitin cewa su sanar da matan da suke aiki a wajensu domin kiyaye al'adar mutanen yankin."

Kara karanta wannan

Mazauna Port Harcourt sun damu da rikicin Wike da Fubara, sun mika bukata ga alkalai

Al'adar bikin Ore dai ta shahara a tsakanin Yarabawa ne musamman wadanda suke Kudancin Najeriya. A lokutan bikin, maza sukan yi ado da rana su zagaye gari tare da kade-kade da raye-raye.

Ore: Hukuma ba ta ce komai ba

Sai dai yunkurin ji ta bakin rundunar yan sandan jihar Legas kan halin da ke ciki a yankin ya gagara

An nemi jin karin haske daga bakin masarautar Ikorodu ma amma basu amsa wayar tarho da aka musu ba.

Gwamnan Bauchi zai bada tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya yi alƙawarin cewa zai ci gaba da tallafawa mutane da kayan abinci har bayan watan azumin Ramadan a Bauchi.

Ƙauran Bauchi ya kuma ja hankalin al'ummar musulmi su kaunaci juna kuma su yi koyi da kyawawan ɗabi'un Annabi Muhammad SAW.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel