Bankin Duniya Ya Lamuncewa Gwamnatin Tinubu Cin Sabon Bashi Na Dala Miliyan 500

Bankin Duniya Ya Lamuncewa Gwamnatin Tinubu Cin Sabon Bashi Na Dala Miliyan 500

  • An amince da sabon bashi na $500m da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta nema
  • Bankin duniya ya amince da bashin ne da nufin tallafawa gwamnati wajen inganta rayuwar mata a Najeriya
  • A cewar rahotanni, bashin $500m shine bashi na biyu da bankin ke lamuncewa gwamnatin Tinubu

Babban bankin Duniya ya amince da bukatar gwamnatin tarayya na cin bashin $500m domin taimakawa Najeriya a shirin tallafawa mata.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, wannan sabon bashin shine bashi na biyu da bankin duniya ke amincewa da shi karkashin sabuwar gwamnati ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Bankin Duniya Ya Lamuncewa Gwamnatin Tinubu Cin Sabon Bashi Na Dala Miliyan 500 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Me yasa bankin duniya ya amince da bashin $500m

A cikin wata sanarwa da ya fitar, bankin duniyan ya ce ya amince da bashin ne domin tallafawa Najeriya a shirin mata, wanda tun da farko aka amince da shi a ranar ranar 27 ga watan Janairun 2018, da kudi $100m

Kara karanta wannan

“Najeriya Na Gab Da Ganin Karshen Rashin Tsaro”, Buni Ya Magantu Kan Nadin Shugabannin Tsaro, Ribadu Da Tinubu Ya Yi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani bangare na sanarwar da bankin duniya ya yi ya ce:

"Bankin duniya ya amince a baiwa Najeriya $500m domin shirin tallafawa mata (NFWP-SU). Wannan kudi zai tallafawa gwamnatin Najeriya wajen zuba jari a shirin inganta rayuwar mata a Najeriya.
"Shirin NFWP-SU zai taimaka wajen tabbatar da mata sun samu damammaki na tattalin arziki masu inganci, wanda yana da matukar muhimmanci don magance matsalar rashin daidaito tsakanin jinsi, samun ilimi mai inganci, lafiya, da sakamakon abinci mai gina jiki ga iyali da kuma karfafa mata da al'ummomi ga sauyin yanayi."

Sai dai kuma bankin duniyan ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin Tinubu ta magance matsalolin da ke hana mata karfin tattalin arziki da kuma kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikinsu.

An ba Tinubu kan wanda zai nada domin gaje Emefiele a matsayin gwamnan CBN

Kara karanta wannan

Adesina Ya Gana Da Tinubu a Paris, Ya Daukarwa Shugaban Najeriya Babban Alkawari 1

An shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi watsi da dabi'ar nan ta nada ma'aikatan banki a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN.

Deji Adeyanju, dan fafutukan Najeriya shine ya bayar da wannan shawara a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter don martani ga kiran da wasu ke yi na baiwa Adesola Adeduntan mukamin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel