“Ban Mutu Ba Lokacin Da Suka Binne Ni”: Wani Mutum Ya Ga Mawaki Mohbad a Mafarki

“Ban Mutu Ba Lokacin Da Suka Binne Ni”: Wani Mutum Ya Ga Mawaki Mohbad a Mafarki

  • Wani dan Najeriya ya wallafa bidiyo a soshiyal midiya yana mai bayyana mafarkin da ya yi da marigayi mawakin nan na Najeriya, Mohbad
  • A wallafarsa mai tsuma zuciya, mutumin ya yi ikirarin cewa mawakin bai mutu ba a lokacin da aka binne shi
  • Matashin ya kuma bayyana cewa dan Mohbad, Liam, zai fara yin abubuwan al'ajabi kafin ya kai shekaru uku a duniya

Wani matashi dan Najeriya ya jaddada cewar marigayi mawakin nan na Najeriya, Mohbad bai mutu ba a lokacin da aka binne shi a harabar gidan mahaifinsa.

Matashin wanda ya yi ikirarin cewa ya yi mafarki, ya ce mawakin ya bayyana abun da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Wani dan Najeriya ya yi mafarki da mawaki Mohbad
“Ban Mutu Ba Lokacin Da Suka Binne Ni”: Wani Mutum Ya Ga Mawaki Mohbad a Mafarki Hoto: @officialkingwhite0/TikTok.
Asali: TikTok

A cewarsa, mawakin bai yi mutuwar Allah ba. Ya yi ikirarin cewa yana nan da ransa har zuwa lokacin da aka binne shi.

Kara karanta wannan

"Sabuwa Fil a Leda": Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

Sako a kan dan Mohbad

Ya bayyana cewa dan mawakin, Liam, zai yi abubuwan ban mamaki kafin ya kai shekaru uku a duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamansa:

"Lokacin da mutane suka ce sun yi mafarki da Mohbad, ban yarda da su ba. A karshe ya bayyana, ya ce ku rike mahaifinsa da kyau. Ya ce bai mutu ba lokacin da aka binne shi, kawai dai yana cikin mafarki ne da kuma tafiyar ceto wasu da ke kangin bauta kawai sai aka kashe ni kafin na farka.
"Shi dan aike ne wanda ya isar da sakonsa ta hanyar wakarsa kuma ya bar wani bangare nasa ta hanyar sake haifo kansa a cikin dansa. Ku rubuta maganganuna ku ajiye, kafin yaron nan ya cika shekaru uku, zai yi abun al'ajabi."

Jama'a sun yi martani kan bidiyon mutumin da ya ga Mohbad a mafarki

Kara karanta wannan

"Ba Aikin Yi": Dan Najeriya Da Ya Koma Canada Neman Rayuwa Mai Kyau, Ya Tattaro Komatsansa Ya Dawo Gida

Jezhi_yaks ya ce:

"Don Allah daga yanzu duk wanda zai yi magana, ya yi amfani da harshen Turanci don Allah, wannan batu ne na kasa baki daya a yanzu ba bau na kabila ba."

Qudee_vybz ya yi martani:

"Na rantse ko ni ina ganinsa. kansa na da karfi sosai."

Qudee_vybz ya kara da cewa:

"Ba ka binne mutum a raye. Za su dawo suna farautar ka."

Official_glory_gee ya ce:

"Bari na yi maku bayani. Ya ce a rike mahaifin Imole cewa mahaifinsa ya san wani abu game da mutuwar dansa kuma cewa Allah ya aiko Imole kuma cewa dan Imole zai maye gurbin Imole nan ba da jimawa ba."

Yaron Da Aka Nemi Hanjinsa Aka Rasa Ya Kwanta Dama

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani yaro mai suna Adebola Akin-Bright, wanda aka nemi hanjinsa aka rasa a yayin da ake masa tiyata ya mutu.

Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, Akin-Bright ya mutu ne a yammacin ranar Talata, 19 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel