Alamu 10 na farko-farko da wadanda suka kamu da kanjamau kan fara ji

Alamu 10 na farko-farko da wadanda suka kamu da kanjamau kan fara ji

- Da yawa daga masu cutar kanjamau sun ara ne da jin wasu, ko duka daga wadannan alamomi

- Cutar HIV ita ce take zama AIDS kuma tana yakar garkuwar jiki mai kare mu daga cututtuka

- Kanjamau dai ba'a santa a da ba, sai shekaru 40 da suka wuce, an gano cewa virus ke jawo ta

Daga alamomi da Legit.ng dai ta binciko muku ka iya zama mutum na kokarin kamuwa da cutar HIV akwai;

1. Zazzabi da yaki ci yaki cinyewa; idan ana jin hakan har makonni bayan shan magani, a je ayi tes na cutar kanjamau.

Alamu 10 na farko-farko da wadanda suka kamu da kanjamau kan fara ji
Alamu 10 na farko-farko da wadanda suka kamu da kanjamau kan fara ji

2. Ciwon makoshi, wanda ake kira sore throat, idan ya hadu da sauran alamu, a binciki lafiya.

3. Kurarraji a fata.

4. Gumin dare bayan mutum na cikin ni'ima

5. Kaluluwa.

DUBA WANNAN: Jiga jigai 7 da ka iya kawar da mulkin APC a zaben 2019

6. Yawan ciwon jiki da gabobi.

7. Gajiya da raki, bayan ba'a yi aikin komai ba.

8. Barkewar zawo.

9. Yawan ciwon kai, maras dalili

10. Amai ko tashin zuciya.

A kula, ba wai kawai don mutum na daya ko biyu daga cikin wadannan wai lallai yana da cutar ba, a'a. Kawai dai idan sun hadar wa mutum farat ta daya a jika, masana kan ce a je ayi bincike, ko a tari cutar da wuri, idan har ita ce.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng