Wike Ya Koma Yi Wa PDP Shakiyanci a Kan Rashin Nasara a Kotun Zaben 2023

Wike Ya Koma Yi Wa PDP Shakiyanci a Kan Rashin Nasara a Kotun Zaben 2023

  • Tun farko Nyesom Wike ya na ganin da kamar wahala a iya ruguza zaben shugaban kasa a kotu
  • Ministan na Abuja ya fadi ra’ayinsa a kan kashin da APM, Atiku Abubakar da Peter Obi su ka sha
  • Wike ya ce karfin halin ‘yan jam’iyyarsa ta PDP ya jawo su ka rika tunani za sui ya karbe mulki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike ya ce bai san wa ya ba jam’iyyar PDP karfin halin tunanin nasara a kotun zaben shugaban kasa ba.

Da aka yi hira da shi a tashar Channels a makon nan, Minista Nyesom Wike ya nuna tun farko bai yi tunanin kotun za ta sauke Bola Tinubu ba.

Tsohon gwamnan na Ribas bai yi mamakin nasarar da APC ta samu a kan PDP, LP har da APM ba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: Atiku Ya Yi Sabon Zargi a Kan Kotun Zaben Shugaban Kasa

Ministan Abuja, Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Nyesom Wike ya yabawa kotu

Yayin da aka zantawa da shi, ‘dan siyasar ya jinjinawa alkalan kotun sauraron karar zaben da su ka tabbatar da hukuncin da INEC ta zartar a Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya na ganin abin da kotun ta zartar dabam da tunanin mutane a shafukan sada zumunta.

Daily Trust da ta saurari tattaunawar ta rahoton ministan ya na zargin ‘yan adawa da magoya bayansu da jahiltar yadda kotun zabe ta ke aikinta.

Matsayar Wike a kan shari'ar zaben 2023

"A lokacin zaman sauraron karar zaben, akwai maganar Shettima a kotun koli. Ban san aikin wanene kuma ya ke ba su duk wani kwarin gwiwa ba.
A shari’ar nan, a matsayin wanda ke cikin majalisar amintattu, na aika sako cewa mu yi addu’a cewa gobe ranar mu ce.
Ban san wanene ya ke ba su duk karfin halin nan ba. Ban sani ba ko fastoci ne ko limamai ba. Ban san wanene ke kyankyasa masu, bai fada masu gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Shari’ar Zabe: Abin da zai faru da PDP da LP idan sun tafi kotun koli – Gwamna Bello

Idan ka saurari shari’ar za ka fahimci irin abin da ake sauraro a dandalin sada zumunta.
Ba su halarci zaman kotun ko na kwana guda ba, amma su na kawo tarkace. Mun komawa yi wa alkalai barazana saboda hukunci ya yi mana dadi.
Na kalli wani bidiyo inda wani fasto ya tattara hoton alkalan a kotu kuma ya bukaci mabiyansa su yi addu’a a kan su.

- Nyesom Wike

An karbe kujerar LP a kotu

An samu rahoto Farfesa Sunday Nnamchi ya na daf da rasa kujerar da yake kai ta ‘dan majalisa mai wakiltar Enugu ta Gabas da Isi-Uzo a Abuja.

Hon. Prince Nnaji ya shigar da kara a kotun zabe kuma ya yi nasara. Alkalai sun tabbatar da Nnamchi bai da hurumin shiga takara a am’iyyar LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel