Tashin Hankali: An Gano Gawar Dalibar Jami'ar Najeriya Da Ta Bace a Wani Yanayi Mai Ban Tausayi

Tashin Hankali: An Gano Gawar Dalibar Jami'ar Najeriya Da Ta Bace a Wani Yanayi Mai Ban Tausayi

  • Hukumomi sun sanar da batan Atanda Modupe Deborah, dalibar jami'ar tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE), a farkon makon nan
  • Daga baya an gano gawar Deborah a cikin wani katon rami da aka binne ta a wani wuri mai nisan mita 30 bayan dakin daukar karatu na malaman jinya a FUOYE
  • Lamarin ya haddasa bakin ciki a makarantar FUOYE da kewaye, inda mutane ke mamakin dalilin da yasa aka kashe matashiyar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ekiti - An tsinci gawar wata dalibar jami'ar tarayya ta Oye Ekiti (FUOYE), Atanda Modupe Deborah.

An ayyana batan Atanda, dalibar sashin kula da jinya wacce ke a mataki na biyu bayan ta fita zuwa aji don yin karatu a daren ranar Litinin, 4 ga watan Satumba.

An gano gawar dalibar da ta bata a jami'ar tarayya
Tashin Hankali: An Gano Gawar Dalibar Jami'ar Najeriya Da Ta Bace a Wani Yanayi Mai Ban Tausayi Hoto: Abdulazeez Afunso, Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Atanda Modupe Deborah: An tsinci dalibar da ta bata a mace

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Zaben da Ɗan Takarar NNPP Ya Samu Nasara a Jihar Kano

A ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, magatakardar jami'ar, Mufutau Ibrahim,ya tabbatar da cewar an gano gawar dalibar, jaridar The Cable ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An tattaro cewa an binne gawar marigayiya Deborah a cikin wani katon rami.

Sanarwar da makarantar ta fitar na cewa:

"Labarin da ke zuwa ma sashin tsaro na jami'ar a yanzu haka ya nuna cewa dalibar da ake magana a kanta ta rasu."

Majalisar wakilai ta yi martani kan kisan dalibar FUOYE

Labarin kisan Deborah ya isa majalisar wakilai, wacce ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa dalibar.

Martanin yan majalisar na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Akin Rotimi, kakakin majalisar wakilan.

Rahoton Vanguard ta nakalto Rotimi yana kira ga gwamnatin jihar Ekiti, hukumomin da abun ya shafa da masu ruwa da tsaki a yankin da su hada kai don tsamo wadanda suka aikata laifin tare da hukunta su.

Kara karanta wannan

Ahaf: Uba Sani ya kama lagon PDP, ya ce shaidun adawa sun nuna shi ya ci zabe

Ba a cire kowani sassa na jikin Deborah ba

A halin da ake ciki, jami'ar FUOYE ta yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa makasan Deborah sun cire wani sassa na jikin ta.

Bayan ganin gawar dalibar, wani rahoto da ba a tabbatar ba ya yi ikirarin cewa wadanda suka kashe ta sun cire idanunta. Sai dai kuma, a cikin sanarwar, hukumar makarantar ta ce sun ziyarci inda aka ajiye gawarta kuma za su iya tabbatar da cewar ba a cire kowani sassa na jikinta ba.

Kwamishinan yan sandan Ekiti ya ba da umurni

Kwamishinan yan sandan jihar Ekiti, CP Ogundare, ya ba da umurnin yin bincike sosai a kan lamarin mutuwar Deborah.

Rundunar yan sandan a cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, ta roki jama'a da su kwantar da hankalinsu sannan ya sha alwashin cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa da don gano masu laifin da hukunta su.

Kara karanta wannan

Halin Yunwa: Dalibi Ya Rasa Ransa Kan Zargin Rashin Wadataccen Abinci Mai Gina Jiki A Wata Makaranta Da Ke Jihar Kano

A wani labarin, mun ji cewa wani hazikin dan Najeriya da ke sana'ar siyar da soyayyen ayaba ya nunawa duniya gidan da yake ginawa.

Mutumin mai suna @adegbengaolusegun ya ce ginin shine gida na uku da ya gina tun bayan da ya fara sana'ar siyar da soyayyen ayaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng