Kotun Musulunci Ta Tura Mutumin Da Ya Lakadawa Mahaifiyarsa Duka Gidan Gyara Hali a Kano

Kotun Musulunci Ta Tura Mutumin Da Ya Lakadawa Mahaifiyarsa Duka Gidan Gyara Hali a Kano

  • Wata kotun shari'ar musulunci ta tura wani matashi gidan gyaran hali a jihare Kano bayan ya aikata mummunan hali kan mahaifiyarsa
  • Muntari Garba ana zarginsa da lakaɗawa mahaifiyarsa dukan tsiya tare da yi mata barazanar kisa
  • Ƴan sanda ne suka gurfanar da Muntari a gaban kotun bisa tuhumomin yin amfani da ƙarfin tuwo da barazanar yin kisa

Jihar Kano - Wata kotun shari'ar musulunci ta jihar Kano, mai zamanta a unguwar Kwana Hudu, ta tsare wani mutum mai suna, Muntari Garba Riminkebe bisa zargin lakaɗawa mahaifiyarsa duka.

Muntari Garba bayan ya lakaɗawa mahaifiyarsa duka, ya kuma yi mata barazanar sheƙa ta zuwa barzahu, cewar rahoton Daily Trust.

Kotu ta tura wani mutumi gidan gyaran hali a Kano
Kotun ta tura wani mutumi gidan gyaran hali a Kano Hoto: Kanoreports.com
Asali: UGC

Muntari Garba, wanda yake zaune a Riminkebe cikin ƙaramar hukumar Nasarawa, ya samu kansa a kotun ne bayan rundunar ƴan sandan jihar Kano gurfanar da shi.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Cafke Rikakkun Miyagu Masu Yawa Da Suka Addabi Mutane a Jihar Adamawa

Laifukan da ake tuhumarsa da su

Rundunar ƴan sandan dai na tuhumar Muntari da yin amfani da ƙarfin tuwo da barazanar yin kisa ga mahaifiyarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Laifukan a cewar ƴan sanda, sun saɓa wa sashe na 165 da 227 na kotun shari'ar musulunci, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Tun da farko dai, mahaifiyarsa ita ce ta kai ƙararsa a wajen ƴan sanda, inda ta ce ɗan na ta yana lakaɗa mata duka da ƙoƙarin halaka ta.

Wanda ake ƙarar dai, ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da su.

Alƙalin kotun, mai shari'a Malam Nura Yusuf Ahmad, ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali sannan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba

An daure ɓarawon shanu a Kano

Kotun shari'ar musulunci ta yanke hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan gyaran hali bayan an same shi dumu-dumu da laifin satar shanu guda biyu.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Babban Lauya Ya Bayyana Dalilin Da Zai Hana Kotun Zaben Shugaban Kasa Yanke Hukunci a Ranar Laraba

Mutumin mai suna Usaini Hamisu mai shekara 45 a duniya, ana zarginsa sa sacw shanu waɗanda kuɗinsu sun kai Naira dubu 700.

Magidanci Ya Maka Surikinsa Kara a Kotu

A wani labarin kuma, wani magidanci ya maka surikansa ƙara a gaban kotun shari'ar musulunci a jihar Kano.

Malam Kabir Muhammad mai shekara 34 a duniya ya kai ƙarar surikan na sa nw a gaban kotun, bisa zargin sun ɗauke masa matarsa ba tare da izninsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel