Yaki Da Ta'addanci: Shugaban Sojojin Najeriya Ya Ce Za Su Dauki Matakai Masu Tsauri a jihar Zamfara

Yaki Da Ta'addanci: Shugaban Sojojin Najeriya Ya Ce Za Su Dauki Matakai Masu Tsauri a jihar Zamfara

  • Babban hafsan sojojin Najeriya Taoreed Lagbaja, ya kai ziyarar aiki jihar Zamfara
  • A yayin ziyarar, ya tattauna da gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare kan muhimman batutuwan tsaro
  • Ya bai wa gwamnan tabbacin cewa nan ba da jimawa ba jami'an soji za su fara farmakar 'yan ta'addan jihar

Gusau, jihar Zamfara - Shugaban Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya tabbatarwa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal cewa nan da ‘yan kwanaki kaɗan jami'ansu za su fara farmakar 'yan ta'addan jihar.

A ziyarar da yake gabatarwa a yankin Arewa maso Yamma, Lagbaja ya ziyarci gwamnan jihar Zamfara inda suka tattauna muhimman batutuwa na tsaro kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Babban hafsan sojojin ƙasa ya ziyarci Dauda Lawal na Zamfar
Lagbaja ya ce kwanan nan za su fara ruwan wuta a kan 'yan ta'addan Zamfara. Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Shugaban sojojin ya bayyana matakan da za su taimaki Zamfara

A cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, mai magana da yawun gwamnan jihar Suleiman Bala Idris, ya bayyana cewa shugaban sojojin ya yi magana kan matakan da za su taimakawa tsaron jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Harin 'Yan Bindiga: Gwamnan Jihar Neja Ya Sanya Labule Da Shugaban Hukumar Sojojin Saman Najeriya, Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ziyarar da babban hafsan sojojin ƙasan ya yi, za ta taimaka wajen ƙarawa jami'an sojin da ke filin daga ƙaimi wajen ganin sun yi abinda ya dace kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

A yayin tattaunawar da suka yi da gwamnan, Laftanal Janar Lagbaja ya tabbatarwa da gwamnan cewa sojoji za su fara ƙaddamar da hare-hare a kan 'yan ta'addan jihar cikin 'yan kwanakin nan.

Matawalle ya caccaki Dauda Lawal kan hare-haren 'yan bindiga a Zamfara

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton sukar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi wa gwamna mai ci Dauda Lawal Dare dangane da matsalar tsaro.

Matawalle ya ce ana samun ƙaruwar hare-hare a jihar saboda rashin neman shawarar tsoffin gwamnoni da gwamna mai ci ke ƙin yi.

Kara karanta wannan

Sojojin Nijar Sun Fadi Mummunan Abinda Zai Samu Najeriya Da Ba Su Yi Juyin Mulki Ba

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da ƙumgiyar 'yan jaridu ta ƙasa (NUJ), reshen jihar Zamfara a Abuja.

Sojoji sun halaka 'yan bindiga 10 a jihar Zamfara

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan 'yan bindiga 10 da dakarun sojin Najeriya suka kashe a jihar Zamfara a wani farmaki da suka kai mu su.

A yayin artabu da sojojin Najeriya, mutane tara da aka sace sun samu damar kuɓuta daga hannun 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel