'Dan Tik Tok ya Kashe Kansa Bisa Kuskure a Idon Mabiyansa Wajen Yin Bidiyo

'Dan Tik Tok ya Kashe Kansa Bisa Kuskure a Idon Mabiyansa Wajen Yin Bidiyo

  • An shiga yanayi mara dadi a birnin Virginia da ke kasar Amurka bayan matashi mai shekaru 17 ya harbe kansa bisa kuskure ya na tsaka da daukar kansa bidiyo
  • Rahotanni sun bayyana matashin dan tiktok din mai suna Rylo Hunch wanda aka gani a wani bidiyo yana wulwula bindigar kafin ya saita ta a kan shi ya fadi nan take
  • Duk da ‘yan sanda a garin sun tabbatar da mutuwar matashi ta hanyar harbi bisa kuskure, amma ba su kama sunan Rylo Hunch ba, sai dai 'yan uwansa sun ce shi ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA- ‘Yan sanda a birnin Virginia da ke kasar Amurka sun tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 17 bayan ya harbe kansa bisa kuskure.

Kara karanta wannan

'Banex Plaza': Soja ya shararawa wata mata mari har ta fada doguwar suma

Har yanzu jami’an tsaron ba su ambaci sunan Rylo Hunch ba, amma ‘yan uwansa sun bayyana cewa shi ne ya mutu.

Rylo Huncho
Dan shekara 17 ya harbe kansa bisa kuskure Hoto: @rylohuncho
Asali: Instagram

New York Post ta wallafa cewa 'yan sandan sun bayyana cewa matashin ya rasu ne bayan ya harbi kansa a kai, inda nan take ya ce ga garinku nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya mutu a dalilin Tik Tok

Tun bayan bullar wani bidiyo inda aka ga matashi Rylo Huncho ya na waka, tare a wasa da bindiga a hannunsa.

Yana cikin wulwula bindigar ne sai ya harbi kansa da ita, kuma nan take ya fadi a gaban kyamara.

Mahaifiyar 'Dan Tik Tok ta gigice

Daily Trust cewa mahaifiyar yaron ta rasa inda za ta sa ranta bayan afkuwar lamarin, domin shi kadai tilo ta Haifa a duniya.

Yanzu haka ‘yan uwan mahaifiyar Rylo sun bude shafin tattarawa mahaifiyar yaron wasu kudi domin taimaka mata.

Kara karanta wannan

Rana dubu ta barawo: 'Yan sanda a jihar Niger sun yi ram da barayin ATM

A rubutun da su ka yi a shafin, sun bayyana cewa mahaifiyar yaron ta sha wahalar sosai wajen rainonsa, wanda mutuwarsa ta jefa ta cikin firgici.

‘Yar TikTok ta maka iyayenta kotu

Mun ba ku labarin yadda wata fitacciyar ‘yar tiktok a Amurka, Kiss Theaz ta maka iyayenta a gaban kotu ta na neman a bi mata hakkinta.

Matar ta zargi iyayenta da yin gaban kansu wajen kawo ta duniya ta tare da sun nemi amincewarta ba, ta nemi su biya ta diyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel