'Yan Bindiga Sun Kaddamar da Mummunar Hari a Plateau, an Kashe Mutane 40

'Yan Bindiga Sun Kaddamar da Mummunar Hari a Plateau, an Kashe Mutane 40

  • Sama da mutane 40 ne 'yan bindiga suka kashe a mummunan harin da suka kai kauyen Zurak da ke jihar Plateau
  • Mazauna yankin sun ce ba su iya kai rahoton faruwar lamarin ga jami'an tsaro ba saboda rashin kyawun hanyar sadarwa
  • A cewar wani shugaban matasan yankin, Sahpi’i Sambo, ‘yan bindigar haye a kan babura sun bude wuta kan mai uwa da wabi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Plateau - Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Zurak da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase a jihar Plateau.

An ce sun kashe mutane sama da 40 ciki har da jami'an tsaron sa-kai na ‘yan banga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a birnin tarayya Abuja, sun gamu da matsala

"Yan bindiga sun kai hari Plateau
'Yan bindiga sun kashe akalla mutane 40 a harin Plateau. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kai hari a Filato

A cewar rahoton Daily Trust, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin, lokacin mutane na gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna yankin sun ce ba su iya kai rahoton faruwar lamarin ba ga jami'an tsaro saboda rashin kyawun hanyar sadarwa a yankin.

"An kashe sama da mutane 40" - Sambo

A cewar wani shugaban matasan yankin, Sahpi’i Sambo, ‘yan fashin sun dura kauyen ne a kan babura dauke da mugayen makamai.

Sahpi’i Sambo ya ce:

“Fiye da mutane 40 ne suka mutu yayin da da dama suka jikkata. Mazauna kauyen sun gudu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da su domin neman mafaka.
"Har ya zuwa jiya jami’an tsaro ba su isa kauyen ba. Abin ya yi muni fiye da tunani."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in kwastam a Abuja

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, bai ce uffan a kan maganar ba duk da cewa an tuntube shi gabanin wallafa wannan rahoton.

An kashe shugaban ‘yan bindiga a Sokoto

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kashe wani rikakken shugaban 'yan bindiga, Bello Hantsi, wanda aka fi sani da Mai Dubu-Dubu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i, ya ce Bello Hantsi ne ya ke jagoranta da kuma ba da makamai ga wasu 'yan bindiga biyar da aka kama a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.