Kwanciyar Aure Mai Kyau Shine Sirrin Tsawon Raina, Inji Tsohuwa Yar Shekaru 102

Kwanciyar Aure Mai Kyau Shine Sirrin Tsawon Raina, Inji Tsohuwa Yar Shekaru 102

  • Wata tsohuwa mai shekaru 102 a duniya, Joyce Jackman ta bayyanawa duniya sirrin da ke tattare da tsawon ranta
  • Joyce ta bayyana cewa tarayya da namiji wanda ya iya gyara shimfida da kyau shine dalilin da yasa ta kai yawan wannan shekaru a duniya
  • Ta tabbatar da lallai ta mori kuruciya da kyau kuma ta samu kwanciyar aure mai inganci daga bangaren sahibinta

Wata mutuniyar kasar Birtaniya mai shekaru 102 a duniya, Joyce Jackman, ta bayyana cewa sirrin tsawon ranta ya ta'allaka ne a kan samun kwanciyar aure mai kyau.

Joyce wacce ta yi bikin cikarta shekaru 102 a duniya a ranar 9 ga watan Mayu ta tabbatar da cewar sirrin tsawon ranta yana da alaka da kwanciya da namiji.

Joyce Jackman, tsohuwa mai shekaru 102
Kwanciyar Aure Mai Kyau Shine Sirrin Tsawon Raina, Inji Tsohuwa Yar Shekaru 102 Hoto: Punch
Asali: UGC

Yayin da take zantawa da ma'aikatan a gidanta da ke Essex, ta ce "kwanciyar aure mai kyau da inibi mai kyau" sune hadin da suka taimaka mani wajen tsawon rai na fiye da shekaru 100.

Kara karanta wannan

Ni Mutum Ne Mai Saurin Fushi, In Ji Gwamna Babagana Zulum

Ina mamaki wai shekaruna 102, Joyce

Da take bikin zagayowar ranar haihuwar tata da iyalinta, tsohuwar shahararriyar mai girkin ta so ace ranar ba zai zo karshe ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Cike da farin ciki, Joyce ta nuna mamakinta cewa za ta iya kaiwa irin wannan shekaru na tsufa.

Ta ce:

"Na ji dadin wannan rana. Na kasa yarda shekaruna 102.
"Shakka babu duk alawar da nake ci ne suka taimaka."

Lokacin da take matashiya, Jackman ta yi aiki a shagon siyar da alawa kafin ta fara aiki da kamfanin Royal Air Force a matsayin mai dafa abinci lokacin yakin duniya na biyu.

Ta auri sahibinta na kuruciya, Terence Jackman, a 1945 lokacin da yakin ya zo karshe, sannan sun ci gaba da rayuwa cikin farin ciki.

Koda dai bata taba haihuwa ba, Jackman na son kula da yaran makwabtanta, tana mai tuna yadda take girke-girke da mahaifiyarta da fita da abokanta.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Wanke Doguwa Daga Zargin Kisan Kai

Da sanyin safe ya fi dacewa ma'aurata su yi kwanciyar aure, bincike

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bincike da aka gudanar a kasar Burtaniya ya nuna cewa ya kamata duk ma'auratan da ke kokarin kara dankon so da jin dadin rayuwar aurensu su dunga kwanciyar aure mintuna 30 bayan sun tashi daga bacci.

Wani kamfanin kula da kiyon lafiya a ƙasar Burtaniya, wanda kwararrun masu binciken lafiya Andy Duckworth da Paul Finnegan suka kafa a 2019 ne ya gano haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel