Bata Bani Hakkina: Matashi Mai Shekaru 20 Ya Koka A Bidiyo Watanni 3 Bayan Aurensa

Bata Bani Hakkina: Matashi Mai Shekaru 20 Ya Koka A Bidiyo Watanni 3 Bayan Aurensa

  • Wani matashi mai shekaru 20 wanda ya angwance da matashiyar budurwa kwanan nan yana tunanin kashe auren nasa
  • A cewar magidancin, zai dauki wannan matakin ne saboda matar tasa taki basa hakkinsa na auratayya
  • Matashin ya yi korafin cewa a duk lokacin da ya nemi hakkinsa sai ta kawo nata uzurin don haka yake neman shawara daga jama’a

Watanni uku bayan daura aurensu da budurwa yar shekaru 17, matashin ya je shafin soshiyal midiya don nuna rashin jin dadinsa game da yadda zamansu ke gudana a gidan aurensu.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a TikTok, matashin mai shekaru 20 ya koaka cewa bait aba sanin matar tasa ‘ya mace ba tun bayan da suka yi aure.

Kara karanta wannan

Kara Tsawo Nake Duk Bayan Wata 3 Ko 4: Wani Dogon Mutum Ya Ba Da Tarihinsa A Wani Bidiyo

Mata da miji
Bata Bani Hakkina: Matashi Mai Shekaru 20 Ya Koka A Bidiyo Watanni 3 Bayan Aurensa Hoto: TikTok/@apito.luxury
Asali: UGC

Ya bayyana cewa a duk lokacin da ya nemeta domin ta bashi hakkinsa, sai ta zo da uzuri.

Matashin wanda shine da daya tilo da iyayensa suka haifa ya bayyana cewa ba zai iya cin amanar matar tasa ba domin yana tsananin sonta sannan ya nemi jama’a su bashi shawara kan matakin da ya kamata ya dauka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Watanni 3 kenan da na auri wannan yarinyar yar shekaru 17.
“Nayi auren wuri ina da shekaru 20 saboda ni kadai ne namiji a gidanmu.
“Tunda na aureta bata bani hakkina na mijinta.
“Kuma ba zan iya cin amanarta ba saboda ina sonta sosai.
“A duk lokacin da na gwada haka sai ta bani uzuri.
“Dan Allah me zanyi saboda na kusa hakura,” ya rubuta.

A wani sako da ya aikewa Legit.ng, matashin ya tabbatar da cewar da gaske ya auri yar shekaru 17 ba wai nean suna yake yi da bidiyonsa ba.

Kara karanta wannan

Dan Achaba Ya Baje Kolin Dankareren Gidan Da Ya Ginawa Mai Shirin Zama Amaryarsa, Hoton Ya Ja Hankali

Yace ya fito daga yankin Ahaizu Mbaise a jihar Imo, haka itama matar tasa amma suna zaune a Owerri.

Game da abun da ya sauya tun bayan korafinsa a yanar gizo, matashiyar matar tasa ta fara bashi kulawa.

Kalli wallafarsa a kasa:

ama'a sun yi martani

gloriaamyloveolis ta ce:

“Ka zaunar da ita gemu da gemu ku tattauna, lallai tana tsoron wani abu ne. kuma kada ka manta ka zamo mai kirki da tattausa kalamanka a gareta.”

user6221505956379 ta ce:

“Da fatan ka san yadda ake lallashin mace saboda nima irin matan nan ne da idan baka lallashe ni ba bana bayarwa.”

NC Designs ta ce:

“Dole ka kaita coci don ayi mata addu’a, tana da miji aljani amma ba laifinta bane dan Allah kayi iya bakin kokarinka..”

user7624750907982 ta ce:

“Akwai matsala a wani wuri, don haka ka zaunar da ita cikin so da kauna don jin ta bakinta.”

Kara karanta wannan

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

Matashi Dan Shekaru 20 Ya Auri Matashiyar Budurwa, Bidiyon Aurensu Ya Haddasa Cece-kuce A Intanet

Mun kawo a baya cewa, wani matashin dan Najeriya mai shekaru 20 ya wallafa bidiyon aurensa da wata yarinya da yayi ikirarin shekarunta 17.

Matashin ya yi alfahari da kasancewarsu ma’aurata mafi karancin shekaru, yana mai cewa sun cancanci shiga kundin tarihu na duniya.

Ya wallafa wani bidiyon shagalin bikinsu wanda aka yi a wata jiha da ke yankin kudu maso gabashin kasar a TikTok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel