Magidanci Ya Koka Kan Yadda Matarsa Da Mahaifiyarta Suka Nemi Su Talauta Shi

Magidanci Ya Koka Kan Yadda Matarsa Da Mahaifiyarta Suka Nemi Su Talauta Shi

  • Ma'aikacin banki ya koka kan yadda matarsa ta hada baki da mahaifiyarta wajen tatsar makudan kudade a hannunsa
  • Ya ce matar tana zambada kudi a duk lokacin da ta je yin sayyaya ta kayayyakin amfanin gida
  • Ya kuma koka kan yadda matar ta hada kai da mahaifiyarta wajen hana shi kara aure

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ibadan jihar Oyo - Wani ma'aikacin banki Biliameen Oyesola, ya nemi wata kotun kostamare da ke zamanta a Ibadan ta raba aurensa da matarsa bisa dalilin tatsar kudade masu yawa daga hannunsa.

Ya shaidawa kotun cewa matar ta sa tana zanbada kudaden cefanen da take karba a hannunsa fiye da tunani, kuma a duk lokacin da ta yi hakan, sai ta tafi wajen mahaifiyarta kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Magidanci ya nemi kotu ta raba aurensu
Magidanci ya koka kan yadda matarsa ke tatsar kudade masu yawa hannunsa. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ta na hada baki da mahaifiyarta wajen tsawwalawa mijin

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Oyesola ya ce a duk lokacin da ya bai wa matar ta sa mai suna Rofiat kudaden da za ta yi sayyaya, sai ta zambada kudin tare da hadin bakin mahaifiyarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kara da cewa a lokacin da ya gano ta ne ya nemi ta rika kawo takardar shaidar biyan kudi na duk abubuwan da ta saya, inda ya ce hakan bai samu ba.

Ya kuma bayyana cewa a lokacin da ta haifi yaronsu na karshe, ta sake hada baki da mahaifiyarta wajen zambada kudaden magungunan da aka rubuta ma ta kafin dawowarsa.

Ya ce bai biya kudaden ba saboda sun gaza kawo masa takardar shaidar biyan kudin da ya nemi su nuna masa.

Matar da mahaifiyarta sun hana shi kara aure

Oyesola ya kuma shaidawa kotun cewa matar tasa ta tsiri wata dabi'a ta barin gidansa ta tafi zuwa gidan mahaifiyarta a kai a kai.

Kara karanta wannan

“Na Samu Kudi Ba Na Wasa Ba”: Budurwa Ta Taka Rawa a Wajen Jana’izar Mahaifinta, Ta Baje Makudan Kudin Da Ta Samu

Ya ce ya gargade ta sannan ya sanya limamin unguwarsu ya shiga cikin lamarin, amma duk da haka ba ta daina ba kamar yadda The Nation ta wallafa.

Ya kuma tabbatarwa kotu cewa matar ta sa da mahaifiyarta sun hana shi kara aure kuma sun hana shi jin dadin wanda yake ciki a yanzu.

Daga karshe Oyesola ya roki kotun ta hannanta masa yaransu guda biyu da ke hannun matar ta sa.

Magidanci ya nemi saki a kotu saboda matarsa na lakada masa duka

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton wani magidanci da ya nemi kotu ta raba shi da matarsa sakamakon dukan da ya ce tana yawan lakada masa.

Ya ce matar ba ta son zaman lafiya sannan kuma ba ta ganin girmansa kuma ba ta girmama iyayensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel