Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutum 100 da Ake Zargi da Aikata Laifuka a Bauchi

Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutum 100 da Ake Zargi da Aikata Laifuka a Bauchi

  • Jami'an yan sandan jihar Bauchi sun samu nasarar damƙe waɗanda ake zargi da aikata muggan laifuka sama da 100 cikin wata guda
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar, Auwal Muhammad, ya ce jami'ai sun kwato makamai masu haɗari daga hannun mutanen
  • Ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin gaban Kotu su girbi abinda suka shuka da zaran an kammala bincike

Bauchi state - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Bauchi ta kama mutane sama da 100 bisa zargin aikata laifuka daban-daban kama daga garkuwa, fashi da wasu muggan laifuka.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Mista Auwal Muhammad, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, 2023 a Bauchi.

Rundunar yan sanda.
Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutum 100 da Ake Zargi da Aikata Laifuka a Bauchi Hoto: thenation
Asali: UGC

Ya ce rundunar ta kwato bindigogi; bindigun hannu da aka ƙirƙira, gatari, wuƙaƙe, kwalabe, da sauransu daga hannun waɗanda ake zargi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Sabon Rikici Ya Ɓalle a Arewacin Najeriya, An Kashe Mutane da Yawa

CP Muhammad ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kamata mu lura cewa matsalar tsaro a cikin al’ummarmu ta zama babban abu mai ban tsoro, kamar garkuwa da mutane, ayyuka 'yan bindiga, fashi da makami, ‘yan daba, cin zarafin da suka danganci jinsi da sauransu."
“A halin yanzu ya zama wajibi mu zauna mu sake duba tsarin aikin mu don magance matsalolin tsaro da ke addabar jiharmu da ƙasa gaba ɗaya."
"Saboda haka, Muna buƙatar amfani da duk wata dabara da muke da ita, ta karfi da ta lalama a ƙoƙarin mu na dakile ayyukan laifuka a jihar."

Ya ce rundunar yan sanda zata ci gaba da gudanar da ayyukan da ya dace kan sahihan bayanan sirri da dabarun magance ta’addanci a jihar Bauchi.

Wane mataki yan sanda zasu ɗauka kan mutanen da take zargin?

"Hakan ya haifar da gagarumar nasara a cikin watan da ake magana a kansa" in ji shi, inda ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

Ya nanata kudurin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetekun na haɗa kai da ‘yan sandan al’umma da na leken asiri don magance matsalolin tsaro a kasar nan, rahoton Ripples ya tattaro.

'Yan Daba Sun Banka Wa Ofishin Kamfen Ɗan Takarar Gwamna Wuta a Jihar Arewa

A wani rahoton kuma Yan bindiga da ake zaton yan daban siyasa ne sun ƙona ofishin kamfen jam'iyyar SDP da ke Lokoja, jihar Kogi.

Shaidu sun ce maharan sun fatattaki jami’an tsaron da ke bakin aiki a ofishin yakin neman zaben, inda daga nan ne suka kona ofishin kamfen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel