Sojoji Sun Yi Ajalin ’Yan Ta’adda Da Masu Garkuwa Yayin Luguden Wuta Sama Da Kasa a Yankuna 3 Na Kasa

Sojoji Sun Yi Ajalin ’Yan Ta’adda Da Masu Garkuwa Yayin Luguden Wuta Sama Da Kasa a Yankuna 3 Na Kasa

  • Rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankuna da daman a kasar
  • Daraktan yada labaran hedikwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba shi ya bayyana a jiya Alhamis 20 ga wata Yuli a Abuja
  • Rundunar ta yi luguden wuta sama da kasa inda ta hallaka su a yankunan Arewa ta Tsakiya da Yamma da kuma Gabashin kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Hedikwatar tsaro ta ce rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji da dama a yankuna uku na kasar.

Daraktan yada labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar Edward Buba shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 20 ga watan Yuli a Abuja.

Rundunar Sojoji Sun Ajalin ’Yan Ta’adda Da Masu Garkuwa Yayin Luguden Wuta Sama Da Kasa a Yankuna 3 Na Kasar
Jami'an Sojoji A Najeriya Sun Ajalin ’Yan Ta’adda Da Masu Garkuwa Yayin Luguden Wuta Sama Da Kasa. Hoto: Facebook.
Asali: UGC

Ya ce sun samu nasarar ce a cikin makwanni biyu a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas, inda ya ce rundunar ta yi luguden wuta ta sama da kasa, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Auren Zaurawa: Mata Sun Ƙyalla, Sun Hango ‘Yan Majalisa da Jagororin Kwankwasiyya

Yadda 'yan ta'adda da dama suka mika wuya ga sojoji

Ya kara da cewa a Arewa maso Gabas rundunar sojin ‘Operation Hadin Kai’ ta hallaka ’yan ta’adda da dama da kama masu ba su bayanan sirri a kananan hukumomin Mafa da Kukawa da kuma Konduga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda da dama sun mika wuya bayan sun sha luguden wuta ta sama da kasa inda suka tabbatar musu cewa su fa sun gaji da wannan akidar tasu.

Buba ya ce a Arewa ta Tsakiya, sundunar ta kai samame maboyar ‘yan bindiga tare da kwato muggan makamai a kananan hukumomin Mangu da kuma Jos ta Kudu a jihar Plateau, Daily Post ta tattaro.

Ta kuma kashe wasu da dama a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina

Sannan rundunar ta kai samame maboyar masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa da kuma karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Kwamushe Shanu Fiye Da 1000 Saboda Dalili Daya Tak, Sun Fadi Me Za Su Yi Da Su

Yayin da a Arewa maso Yamma, kakakin hedikwatar tsaron ya bayyana rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ ta kai samame a maboyar ‘yan fashin daji a kauyuka da dama a kananan hukumomi daban-daban, cewar THISDAY.

Ya ce rundunar ta yi luguden wuta ta sama akan ‘yan bindigan tare da hallaka wasu a kananan hukumomin Batsari da Tangaza da kuma Maru da ke jihohin Katsina da Sokoto da kuma Zamfara.

Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Luguden Wuta Kan Mafakar Yan Ta'adda A Kaduna

A wani labarin, rundunar sojin sama ta yi luguden wuta akan mafakar 'yan bindiga da dama a jihar Kaduna.

Harin ya yi sanadin mutuwar 'yan bindiga da dama a kananan hukumomin Chikun da Igabi da kuma Birnin Gwari.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 7 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.