Gwamnan Jihar Zamfara Ya Sanar Da Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu a Jihar

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Sanar Da Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu a Jihar

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci
  • Sanarwar gwamnan ta bayar da hutu a irin wannan ranar al'ada ce wacce aka saba a jihar domin murnar zagoyowar shekarar musulunci
  • Lawal, a cikin wata sanarwa ta hannun, Abubakar Muhammad Tsafe, ya buƙaci al'ummar jihar da su yi addu'ar dawowar zaman lafiya a jihar da Najeriya baki ɗaya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gusau, Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu, domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.

Sanarwar na zuwa ne biyo bayan al'adar gwamnatin jihar ta bayyana ranar 1 ga watan Muharram na kowace shekara a matsayin ranar hutu a jihar, rahoton TVC ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Babbake Fadar Babban Basarake Mai Daraja a Najeriya

Gwamnan Zamfara ya bayar da hutun sabuwar shekara
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutu Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamnan Zamfara ya ci gaba da al'adar jihar

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da darektan ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Muhammad Tsafe, ya rattaɓawa hannu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar sanarwar, gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya buƙaci jama'ar jihar da su gudanar da adddu'o'in dawowar zaman lafiya a ƙasa a wannan lokacin.

Gwamna Lawal ya yi wa al'ummar Musulmai barka da shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.

Idan ba a manta ba dai, mai martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III, ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya sanar da ranar Laraba ne a matsayin 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah, sakamakon rashin ganin jinjirin watan a ranar Litinin 29 ga watan Dhul Hijjah, wanda hakan ya sanya ranar Talata ta zama 30 ga watan Dhul Hijjah, 1444.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP Ya Ayyana Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu, Ya Bayyana Dalili

Ranar Laraba Ta Zama Ranar Hutu a Jihar Osun

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Osun Ademola Nuruddeen Jackson Adeleke, ya sanar da ranar Laraba a matsayin ranar hutu a jihar ta Osun.

Gwamna Adeleke ya bayar da sanarwar ne domin murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel