Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Samar da Abinci a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Samar da Abinci a Najeriya

  • Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan batun tsaron samar da abinci a Najeriya
  • Ya kuma bada umarnin a gaggauta buɗe rumbun gwamnati, a fito takin zamani da hatsi a rabawa manoma da magidanta a ƙasar nan
  • Shugaban ƙasan ya ce gwamnati zata ɗauki matakan da zasu daidaita da sauke farashin kayan abinci daidai aljihun talakawa

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana ta ɓaci kan tsamar da isasshen abinci a Najeriya.

Kakakin shugaban ƙasa, Dele Alake ne ya bayyana haka yayin zantawa da masu ɗauko rahoton gidan gwamnati ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, 2023.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Tsaron Abinci a Najeriya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban kasan ya bada umarnin cewa duk wasu batutuwa da suka shafi abinci da samar da ruwan sha da sauke farashi a maida su karkashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Dalla-Dalla: Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya

Wannan umarni na cikin shirin gwamnatin Bola Tinubu na tabbatar da cewa talakawa masu karamin karfi suna iya dogaro da kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, shugaban kasan ya umarci a gaggauta fitar da takin zamani da hatsi a raba wa manoma da magidanta domin rage musu zafin raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Tinubu ya ɗauki matakan sauke farashin kayan abinci

Hadimin shugaban ƙasa, D. Olusegun ya wallafa cikakkiyar hirar shafinsa na Tuwita. Dele Alake ya ce:

"Dole ma'aikatar noma da ma'aikatar ruwa su hanzarta haɗa kai wajen tabbatar da an samun isasshen ruwa a gonaki da kuma tabbatar da ana samar da abinci a kowane lokaci cikin shekara."
"Zamu kirkiro da kuma goyon bayan hukumar kayyakin abinci wacce zata sa ido, nazari da kuma bibiyar farashin kayan abinci. Haka nan hukumar zata riƙa killace abinci da nufin amfani da su a matsayin makamin saita farashi."

Kara karanta wannan

Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

"Ta hannun wannan hukumar, gwamnati zata shiga ta yi ruwa da tsaki wajen saita tashi da saukar farashin kayayyakin abinci a Najeriya."

Haka zalika ya ƙara da cewa gwamnati zata shigo da hukumomin tsaro cikin batun abinci domin tsare gonaki da manoma ta yadda aikin noma zai kankama ba tare da tsoron hari ba.

Gwamnan Jigawa Umar Namadi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 16

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 16 da ya naɗa a majalisar zartarwa.

Namadi ya buƙaci kwamoshinoni su yi aiki bisa tsoron Allah, gaskiya da riƙon amanar al'umma da kuma sauke haƙƙi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel