Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

  • ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun amince da wata wasikar da shugaban kasa ya aiko masu a jiya
  • Bola Ahmed Tinubu ya nemi a ba gwamnatinsa damar kashe wasu N819bn da ba su cikin kasafin kudi
  • ‘Yan majalisa za su amfana da Naira biliyan 70 daga ciki, talakawa za su samu Naira rabin Tiriliyan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A ranar Alhamis aka samu labari majalisar wakilan tarayya ta amince ayi wa kudirin kundin kasafin kudi na 2022 kwaskwarima.

The Cable ta ce nan take majalisar tarayya ta amince da kudirin da ya fito daga fadar shugaban kasa ba tare da wata doguwar muhawara ba.

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Honarabul Julius Ihonvbere ya gabatar da rahoton da sauran abokan aikinsa duka su ka yi na’am da shi.

Kara karanta wannan

Shugaban Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Batun Samar da Abinci a Najeriya, Ya Bada Sabon Umarni

Majalisar Wakilai
Shugaban majalisar Wakilai a Abuja Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

'Yan majalisa shar a sabon kasafi

Da yake magana a dazu, Benjamin Kalu ya ce an yi la’akari da kalubalen da Sanatoci da takwarorinsa su ke fuskanta cikin karin kasafin kudin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mataimakin shugaban majalisar ya shaidawa zauren, gwamnati za ta duba lamarin walwalarsu da sauran matsalolin da suke samu a bakin aiki.

Yadda za a kashe N819bn a 2023

Bola Tinubu ya bukaci a amincewa gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 819, kaso mafi tsoka za su tafi wajen rage radadin tsadar man fetur.

Awanni bayan wasikar shugaban kasar ta iso majalisar tarayyan, sai aka ji an amince da ita.

A cikin karin wadannan kudi da za a kashe, Daily Trust ta ce an warewa ma’aikatar ayyuka da gidaje Naira biliyan 185 saboda matsalar ambaliya.

Ma’aikatar gona za ta samu Naira biliyan 19.2 da nufin agazawa manoman da suka yi asara a sanadiyyar ambaliyar ruwa da aka yi a shekrar bara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Ciyo Bashin Biliyan 500 Don Ragewa Yan Najeriya Radadi

Muhimman ayyukan da FCTA za tayi za su ci Naira biliyan 10, daga nan aka ware Naira biliyan 70 da sunan gudumuwa domin inganta aikin majalisa.

A halin yanzu mutane da-dama su na kukan ya kamata gwamnati ta rage yawan kudin da ta ke kashewa, ‘yan majalisar kuma su na kukan rashi.

An yi rabon kwamitoci a majalisa

Kafin nan, rahoto ya zo cewa Sanata Asuquo Ekpenyong mai shekara 39 ya zama mataimakin shugaban kwamitin tsaro na kasa a rabon da aka yi.

Sanata Khalid Ibrahim Mustapha ya shiga majalisa da kafar dama, ya samu rikon kwamiti tare da rinsu Sunday Karimi da Williams Eteng Jonah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel