“Akwai Yiwuwar Ministan Kudi Ya Fito Daga Lagas”: Inji Lauya

“Akwai Yiwuwar Ministan Kudi Ya Fito Daga Lagas”: Inji Lauya

  • Akwai yiwuwar ministan kudin shugaban kasa Bola Tinubu zai fito ne daga jihar Lagas
  • Wani lauya mai suna Wale Adeagbo ne ya bayyana hakan ga Legit.ng cewa ya samu labari ne daga wani babban jigon APC a Ikorodu, jihar Lagas
  • Ana sa ran shugaban kasar zai bayyana jerin ministocinsa sannan ya gabatar da sunansu zuwa ga majalisar dattawa a rana ko kafin 28 ga watan Yuli

Ikorodu, Lagos - An tattaro cewa Shugaban kasa Bola Tinubu yana tunanin zabo ministan kudi daga jihar Lagas.

Wani lauya mazaunin Lagas, Wale Adeagbo, ne ya sanar da haka a wata hira ta musamman da Legit.ng ta yi da shi.

Shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu
“Akwai Yiwuwar Ministan Kudi Ya Fito Daga Lagas”: Inji Lauya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ministan kudin shugaban kasa Tinubu

Adeagbo ya ce wata majiya abun dogaro ta fada masa cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

"Akwai yiwuwar ministan kudi zai fito ne daga Lagas."

Ya kara da cewar:

"Wani babban jigon jam'iyyar APC daga Ikorodu ne ya bayyana haka."

Ana sa ran shugaban kasa Tinubu zai mika sunayen ministocinsa ga majalisar dattawa a ranar ko kafin 28 ga watan Yuli, lokacin da zai cika kwanaki 60 a kan karagar mulki.

An tattaro cewa tuni wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka fara kamun kafa domin shiga jerin ministoci a gwamnatin Shugaban Kasa Tinubu.

Tsoffin gwamnoni, tsoffin ministoci na zawarci kujerun ministoci

An rahoto cewa manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da tsoffin gwamnoni, tsoffin ministoci da sauran jiga-jigan APC, sun je gidan Shugaban kasar da ke Bourdillon a Lagas lokacin da Tinubu ya je hutun babban sallah na tsawon kwanaki hudu.

Da farko shugaban kasa Tinubu ya bayyana shirinsa na tafiyar da gwamnati mai hadin kai, inda za a baiwa jiga-jigan jam’iyyun adawa wasu mukamai na minista.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC Ta Fitar da Sanatoci, ‘Yan Majalisa da Za a Warewa Sauran Mukamai 8

Yan siyasa da dama sun bayyana ra'ayoyinsu daban-daban kan shirin shugaban kasar; yayin da wasu suka gargadi Tinubu a kan wannan yunkuri nasa, wasu kuma sun yi amanna da ci gaban, yana mai cewa cancanta ake dubawa.

Shugaban kasa Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan PDP

A wani labari, mun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawar sirri da wasu tsoffin jigan-jigan jam'iyyar PDP biyu.

Shugaban kasar na sa labule da tsohon shugaban majalisar dattawa, Chief Pius Anyim da tsohon kakakin PDP na kasa, Olisa Metuh a fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel