Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano Ta Kama Kwamishinan Ganduje Da Wasu Kan Badakalar Biliyan 1

Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano Ta Kama Kwamishinan Ganduje Da Wasu Kan Badakalar Biliyan 1

  • Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta damke kwamishinan ayyuka na zamanin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje
  • An dai kama Injiniya Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar kan zargin wawure kudi naira biliyan daya da sunan gyara tituna
  • Bincike da hukumar yaki da rashawar ta gudanar ya nuna sam ba a yi aikin gyaran kowani titi ba sannan ba a bi ka'ida ba wajen fitar da kudin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafe ta jihar Kano ta kama tsohon kwamishinan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan badakalar naira biliyan daya, jaridar Aminiya ta rahoto.

Shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar da aka dawo da shi, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya yi alkawarin cewa duk wadanda ake zargi da aikata cin hanci da rashawa sai sun biya bashin abubuwan da suka aikata.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Gangwaje Alhazan Jihar Kano, Ya Ba Su Kyautar Miliyan 65

Tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje
Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kano Ta Kama Kwamishinan Ganduje Da Wasu Kan Badakalar Biliyan N1 Hoto: Punch
Asali: UGC

Wannan ya yi sanadiyar kamawa da tsare tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa, Injiniya Idris Wada Saleh da wasu mutane biyar kan zargin wawure naira biliyan 1.

An fitar da kudin da sunan kwangilar gyaran tituna amma ba a yi ba, bincike

An kama tsohon kwamishinan wanda ya kasance Manajan Darakta na hukumar kula da hanyoyin Kano, sakataren din-din-din, shugaban hukumar kula da harkokin gwamnati , Mustapha Madaki Huguma, daraktan kudi, daraktan bincike da tsare-tsare, da sauransu a yammacin Litinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda jaridar Daily Post ta rahoto, an kama su ne bisa zargin cire kudi sama da naira biliyan 1 domin gyara tituna 30 da magudanar ruwa a cikin birnin, ayyukan da ake zargin ba a aiwatar ba.

Wata majiya a hukumar ta bayyana cewa an biya kudaden da aka cire a rukuni uku cikin asusun kamfanoni uku a watan Afrilun 2023.

Kara karanta wannan

Miyetti Allah Ta Nemi a Saki Mambobinta Da Aka Tsare a Anambra Ba Tare Da Sun Aikata Laifi Ba

“Abin mamaki har hukumar kula da harkokin gwamnati ta bayar da takardar shaidar bayar da kwangilar bayan an biya kudin tun kwanaki goma da suka gabata wanda ya sabawa dokar sayan kayayyaki ta 2021.
"Ofishin bin tsarin ya ce sun ba da takardar shaidar amincewar ne saboda hukumar kula da hanyoyi na Kano ta ce za a gudanar da ayyukan gyara hanyoyin ne ta hanyar amfani da leburori hanyar kai tsaye amma takardun sun nuna akasin haka.

Kakakin hukumar, Abba Kabir, ya tabbatar da cewar wadanda aka kama suna amsa tambayoyi kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da daure wani dan damfara na tsawon shekaru 235

A wani labari na daban, kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin da kotun kasa ta yankewa wani matashi dan damfara.

An yankewa matashin mai suna Scales Olatunji hukuncin daurin shekaru 235 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng