Gwamnan Jihar Yobe Ya Tuna Da Alhazan Jihar a Saudiyya, Ya Yi Musu Gagarumar Kyauta

Gwamnan Jihar Yobe Ya Tuna Da Alhazan Jihar a Saudiyya, Ya Yi Musu Gagarumar Kyauta

  • Gwamnan jihar Yobe ya gwangwaje Alhazan jihar da kyautar makuɗan kuɗi har Riyal 300 a ƙasa mai tsarki
  • Gwamna Mai Mala Buni ya ba Alhazan kyautar kuɗin ne domin rage ɗawainiyoyin da su ke yi yayin Hajjin Bana
  • Alhazan sun yaba da kyautar da gwamnan ya yi musu inda suka yi addu'o'i na musamman ga jihar da ƙasa baki ɗaya a ranar Arafat

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Saudiyya - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ba Alhazan jihar kyautar Riyal 300 kowannensu a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Alhazan jihar 2,018 ne suka samu kyautar da gwamnan ya yi a ƙasa mai tsarki lokacin gudanar da aikin Hajjin na bana.

Gwamnan Yobe ya ba Alhazan jihar kyautar Riyal 300
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Kyautar kuɗin da gwamnan ya ba Alhazan ya bayar da ita ne domin taimaka musu wajen siyan abun Hadaya da rage sauran ɗawainiyoyin da su ke yi wajen aikin Hajjin a ƙasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Makudan Kudade, Ya Daukar Musu Muhimman Alkawura 3

Ɗaya daga cikin mahajjatan, Hajiya Hafsat Umar, ita ce ta bayyana hakan yayin wata hira da jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhazan sun yaba sosai da kyautar da gwamnan ya yi musu

A cewarta Alhazan na jihar Yobe sun yaba da wannan kyautar da gwamnan ya yi musu inda suka mayar da biki ta hanyar yin addu'o'i na musamman a ranar Arafat ga jihar da Najeriya baki ɗaya.

Idan ba a manta ba dai, hukumar jindaɗin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ba hukumar jindaɗin Alhazan jihar Yobe, kyautar hukumar Alhazan jiha da ta fi kowacce ƙwazo a aikin Hajjin shekarar 2022.

Kyautar an bayar da ita ne bayan kwamitin bayar da kyauta na aikin Hajjin shekarar 2022 ya gabatar da rahotonsa, inda ya sanya jihar a mataki na farko a wajen gudanar da ayyuka yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Jerin Ministocin da Tinubu Zai Naɗa? Gaskiya Ta Bayyana

Ko a shekarar da ta gabata, gwamna Mai Mala Buni, sai da ya ba Alhazan jihar kyautar kuɗi domin ya tallafa musu.

Gwamnan Jihar Niger Ya Gwangwaje Alhazan Jihar Da Kyautar Kudi

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Niger Mohammed Umaru Bago, yaba Alhazan jihar kyautar maƙudan kuɗi a ƙasa mai tsarki.

Gwamnan yaba kowannensu kyautar Riyal 100 sannan ya yaba da halin dattako da suka nuna wajen gudanar da aikin Hajjin na bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel