‘Na Yi Ne Don Kwato Kadarorin Gwamnati’: Abba Gida-Gida Ya Tsaya Kyam, Ya Ce Rusau Ba Gudu Ba Ja da Baya

‘Na Yi Ne Don Kwato Kadarorin Gwamnati’: Abba Gida-Gida Ya Tsaya Kyam, Ya Ce Rusau Ba Gudu Ba Ja da Baya

  • Abba Gida-Gida ya bayyana gaskiyar dalilin da yasa yake yawan rushe-rushe a jihar Kano tun bayan hawansa mulki
  • Abba ya tarbi majalisar masarautun Kano a gidan gwamnati a lokacin da suka kai masa ziyarar bikin sallah
  • Ya kuma bayyana irin nasarorin da ya samu daga hawansa mulki zuwa wannan lokacin da ya cika wata guda

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya ba da hujjarsa ta aikin rusa gine-gine da gwamnatinsa ta fara tun bayan hawansa karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, Channels Tv ta ruwaito.

Da yake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na gudanar da aikin yayin bikin Sallah, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa yana aikin rusau ne domin kwato kadarorin jama’a kuma mallakin gwamnati.

Dalilin da yasa nake rushe-rushe a Kano
Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Kano | Hoto: Kwankwasiya Reporters
Asali: Facebook

Dalilin yin rusau a Kano

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Hisham Habib ya fitar, ta ce Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin kwato kadarorin gwamnati da wasu daidaikun mutane da shafaffu da mai a gwamnatin Ganduje suka mallaka ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Dalilinmu Na Ruguza Gine-Gine a Jihar Kano – Abba Ya Ce Bai Yi Nadamar Komai ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga mai martaba sarkin Kano a ziyarar gaisuwar Sallah, ya ce:

“Mai martaba, yana da kyau majalisar masarauta ta lura cewa mun fara aikin rusau ne domin kwato kadarorin gwamnati da aka mallakarwa wasu ba bisa ka’ida ba, kuma za mu tabbatar da cewa an dawo da duk wadannan kadarorin domin amfanin mutanen Kano."

Irin nasarorin da aka samu a mulkin Abba Gida-Gida

Gwamnan ya nuna jin dadinsa ga mai martaba sarkin da majalisar masarautun Kano bisa ziyarar da suka kai masa, inda ya bayyana cewa wannan ita ce ziyara ta farko da ya samu tun bayan hawansa mulki.

Ya yi amfani da damar wajen bayyana nasarori da dama da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 31 da suka gabata, rahoton Vanguard.

Tun bayan hawan Abba Gida-Gida ake ci gaba da cece-kuce da maganganun ra'ayoyi kan rusau da yake yawan yi a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: NLC Za Ta Shiga Takun Saka Da Abba Gida Gida Kan Albashin Ma’aikata Fiye Da 10,000

Abba Gida-Gida ya rushe sha-tale-take a Kano

A wani labarin, kun ji yadda Kanawa suka tashi da ganin yadda Abba Gida-Gida ya rusa daya daga cikin sha-tale-talen da ake ji dasu a jihar Kano.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ke ci gaba da ikrarin cewa, yana aiki ne don tabbatar da kwato kadarorin gwamnatin jihar.

Ana ci gaba da cece-kuce game da ayyukan rusau da Abba Gida-Gida ke yi a jihar tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel