Amfanin Albasa 5 a jikin dan adam

Amfanin Albasa 5 a jikin dan adam

Albasa na da tarin alfanu a cikin jikin dan adam, sannan kuma an dade ana amfani da albasa wajen magani cututtuka da dama.

Baya ga haka albasa na karawa abinci dandano da kamshi mai dadi, wadda ake ganin yana daga cikin muhimman sinadarai na yin girki.

Don haka muka kawo maku wasu daga cikin alfanun da albasa ked a shi a jikin dan adam.

Amfanin Albasa 5 a jikin dan adam
Amfanin Albasa 5 a jikin dan adam

Ga su kamar haka:

1. Albasa na taimakawa sosai wajen maganin sanyi, sai daimutane da dama basu san cewa wannan sinadari na maganin ciwon tarin fuka da jiri ba.

2. Cin albasa cikin abinci na taimakawa wajen wanke jinin jikin dan adam ta yadda zai kore duk wani dauda dake tattare da jinin.

3. Ana amfani da albasa wajen gyaran fuska sakamakon sinadarin ‘carotene’ da yake tattare da shi.

4. Albasa na taimakawa wajen kare jikin dan adam daga kamuwa da cuta sannan yana warkar da cuta na ciki da wajen jikin bil’adama idan ana ta’ammali da cin sa sosai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mahaifiyar Gwamna Dickson ta mutu bayan fama da cutar daji

5. Albasa na taimakawa grkuwar jikin namiji ta yadda zai samu Karin kuzari musamman ta bangaren auratayya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng