Na Kashe Sama Da Biliyan 20 Kan Tallafin Karatu, Ganduje Ya Mayar Wa Abba Gida-Gida Martani

Na Kashe Sama Da Biliyan 20 Kan Tallafin Karatu, Ganduje Ya Mayar Wa Abba Gida-Gida Martani

  • Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta iƙirarin da sabon gwamna Abba Gida Gida ya yi, na cewa an daina ba da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje a karkashin gwamnatinsa
  • Ganduje ya ce ya kashe sama da naira biliyan 20 ga ɗalibai 111,687 domin zuwa ƙaro karatu zuwa ƙasashen waje dama nan cikin gida Najeriya daga watan Yunin 2015 zuwa watan Maris na 2023
  • Ganduje ya kuma ce ya biya kaso mai tsoka na bashin da gwamnatin Kwankwaso ta bari, wanda ya kai kimanin dala miliyan 28 da sama da naira biliyan 6, kafin ƙarewar wa'adinsa a ranar 29 ga watan Mayu

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta iƙirarin da gwamna mai ci a yanzu, Abba Kabir Yusuf da ake wa lakabi da Abba Gida Gida ya yi, na cewa an daina ba da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje a karkashin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Babban Jigon da Alamu Suka Nuna Zai Koma APC, Ya Roƙe Shi Alfarma 1

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta kashe fiye da naira biliyan 20 ga dalibai 111,687 don ƙaro karatu a ƙasashen waje 14, jami’o’i masu zaman kansu guda biyar, makarantar shari’a ta Najeriya da sauran jami’o’in cikin gida daga watan Yunin 2015 zuwa Maris na 2023.

Ganduje ya yi wa Abba Gida Gida martani kan tallafin karatu
Ganduje ya ce ya kashe sama da N20b wajen tallafin karatu ga ɗaliban jihar Kano. Hoto: Gida Gida TV
Asali: Facebook

Abba Gida Gida ya sanar da dawo da tallafin karatu ga ɗaliban Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa, Abba Gida Gida ya yi iƙirarin ne a ranar Juma’ar da ta gabata a yayin da yake sanar da cewa gwamnatinsa ta dawo da shirin ba da tallafin karatu ga daliban da suka kammala digiri da sakamako mafi daraja, don ci gaba da digiri na biyu a jami’o’in cikin gida da na kasashen waje.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abba ya bayyana cewa ba a ƙara bayar da tallafin ba tun bayan shekarar 2015, wato lokacin gwamnatin injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Sabon Gwamna Ya Sake Fito da Tsarin Zuwa Jami’o’in Kasashen Waje

Da yake mayar da martani a wata sanarwa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida a gwamnatin, Muhammad Garba ya fitar, Ganduje ya ce abin takaici ne yadda gwamna Abba Kabir ke kawo maganar gwamnatin Kwankwaso.

Ganduje ya ce gwamnatin ta bar bashin kusan dala miliyan 28, da kuma sama da naira biliyan 6, wanda a cewarsa gwamnatinsa ta biya wani ɓangare mai tsoka kafin ta bar ofis a ranar 29 ga watan Mayu.

Ya bayyana cewa sama da Naira biliyan 20 da gwamnatinsa ta kashe wajen bayar da tallafin karatu na digiri na biyu a kasashen waje, ya ƙunshi kuɗaɗen karatu, kula da ɗalibai, wurin kwana, tikitin jirgin sama, da dai sauransu.

Ya ƙara da cewa an ware kuɗaɗen ne ga ɗaliban da suka kammala karatun digiri na biyu a ƙasashen waje irinsu Indiya, Malaysia, Masar, Cyprus, China, Turkiyya, Uganda, Birtaniya, Togo, Ireland, Gambia, Ukraine da ma jami'o'in cikin gida.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Jerin Muhimman Abubuwa 8 Da Gwamnatinsa Za Ta Mayar Da Hankali A Kai

Ganduje ya tura malaman jami'o'i 50 ƙaro karatu a ƙasashen waje

Sannan ya ce tsohuwar gwamnatin ta kuma ɗauki nauyin malamai 50 daga jami’o’inta guda biyu da sauran manyan makarantu don su yo digirin digirgir a manyan jami’o’in Faransa a karkashin wani shiri da aka yi a tsakanin gwamnatin Faransa da ta Kano.

Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa, gwamnatin ta Ganduje ta sake dawo da biyan kuɗaɗen alawus ga ɗalibai ‘yan asalin jihar Kano da ke karatu a jami’o’in Najeriya da sauran manyan makarantun gaba sakandire, shirin da gwamnatin Kwankwaso ta yi watsi da shi a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Ya ce gwamnatin ta Ganduje ta kuma ƙara yawan kuɗaɗen alawus ɗin da take bai wa ɗaliban da kaso 50 cikin 100, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Muƙamin da ake tunanin Tinubu zai bai wa Kwankwaso

A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoto kan muƙamin da majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa Tinubu zai bai wa Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna APC Ba Shi Da Lafiya, Ya Miƙa Mulki Ga Mataimakinsa Ya Tafi Ƙasar Waje Ganin Likita

Majiyar ta bayyana cewa Tinubu na shirin bai wa ɗan takarar shugabancin ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar NNPP muƙamin ministan tsaro na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel