Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

  • Kakakin DSS ya fitar da sanarwa cewa akwai yiwuwar ‘yan ta’adda su kai hare-hare kwanan nan
  • Hukumar tsaron ta na zargin ana shirin yin ta’adi a lokacin da ake shiryawa bukukuwan sallah
  • Dr. Peter Afunanya ya ce DSS da Sojoji da ‘Yan Sanda sun bankado mummunan tanadin miyagu

Abuja - Hukumar DSS ta ankarar da al’umma cewa akwai shirye-shirye da wasu miyagu su ke yi na kai wa wuraren bauta da filayen wasanni hari.

A rahoton da aka samu daga Punch a ranar Juma’a, an fahimci cewa ana yunkurin kai hare-haren ne a lokuta da kuma kafin bukukuwan babbar sallah.

Mai magana da yawun bakin DSS a Najeriya, Dr. Peter Afunanya ya yi kira ga masu manyan shaguna su kara sa ido a daidai lokacin nan da aka shiga.

Kara karanta wannan

Ciki Ya Ɗuri Ruwa, DSS Sun Je Gidan Abdulrasheed Bawa, An Zurfafa Binciken EFCC

Jami'an Hukumar DSS
Jami'an Hukumar DSS Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano makamin IED

Peter Afunanya ya shaida cewa jami’an tsaro masu fararen kaya da dakarun ‘yan sanda da sojoji sun yi nasarar gano wasu makaman IED masu tashi.

Bama-baman da ake shirin tadawa su ka haskawa jami’an tsaro ana niyyar ta’adi.

An rahoto Afunanya ya na bada shawarar cewa jama’a su yi gaggawar ankarar da jami’an tsaro da zarar sun ci karo da wasu mutanen da ba a sani ba.

Hukumar DSS ta na kira da a sa ido kafin bukukuwan Sallah musamman da rahotanni su ka zo cewa ana so a kai hari a dakunan bauta da wuraren shakatawa kafin da bayan bukukuwan.

Wannan ya bayyana ne bayan gano wasu makaman IEDs da ake zargin ‘yan ta’adda sun kafa.

Ana yin kira ga shugabanni da masu kula da wuraren taron jama’a har da kasuwanni, shaguna da sauransu da su sa ido kuma su kai karar duk wani motsi ko mutanen da ba a gane kan su ba.

Kara karanta wannan

An Bude Iyakar Legas Domin Shigo da Motoci, Gwamnati Ta Yi Watsi da Tsohon Tsari

ICRI ta ce jami’an tsaron masu fararen kaya sun yi alkawarin hada-kai da duk wasu jami’an tsaron da ke kasar nan domin ganin an yi maganin ‘yan ta’adda.

Ana binciken Shugaban EFCC

A rahoton da mu ka samu a makon nan, an ji cewa yayin da ya shafe tsawon mako daya yana tsare, binciken DSS ya kai ga na kusa da AbdulRasheed Bawa.

Har gida aka je aka iske mai daki da yaran Bawa, aka rika lalube bayan an tsefe ofishinsa, sannan na hannun daman shugaban EFCC sun amsa tambayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng