Manjo Janar Lagbaja Ya Kama Aiki a Matsayin Shugaban Sojin Ƙasa Na 23

Manjo Janar Lagbaja Ya Kama Aiki a Matsayin Shugaban Sojin Ƙasa Na 23

  • Sabon hafsan sojin kasan Najeriya, COAS Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya kama aiki a matsayin shugaban soji na 23 ranar Jumu'a a Abuja
  • Ya ɗauki alkawarin cewa zai yi duk mai yuwuwa wajen ganin ya sauke nauyin da ke kansa cikin adalci
  • Tsohon COAS, Farouk Yahaya, ya ce zai bar hukumar soji fiye da yadda ya same ta kuma ta samu manyan nasarori a karkashin kulawarsa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Sabon shugaban rundunar sojin ƙasan Najeriya (COAS), Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya kama aiki a matsayin shugaban sojin na 23 a tarihi.

Sabon shugaban rundunar sojin ya sha alwashin cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen sauke nauye-nauyen da ke kansa tare da yi wa kowa adalci, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sabon shugaban sojin Najeriya, COAS Lagbaja.
Manjo Janar Lagbaja Ya Kama Aiki a Matsayin Shugaban Sojin Ƙasa Na 23 Hoto: News in Nigeria/facebook
Asali: Facebook

Shugaban hukumar sojin ƙasa na 22, Janar Faruk Yahaya mai ritaya ne ya miƙa masa alamar karɓar ragama a wani biki da aka shirya a hedkwatar sojoji da ke Abuja ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro Ta Zo Karshe, Sabon Shugaban Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ne ya naɗa Lagbaja a matsayin hafsan sojin ƙasa da yammacin ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023 bayan ya sauke baki ɗaya hafsoshin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, Manjo Janar Lagbaja ya ɗauki alkawarin cewa zai ɗora daga inda Yahaya ya tsaya wajen gina jajirtacciyar rundunar soji.

Bugu da ƙari sabon COAS ɗin ya bayyana cewa ba zai riƙa barin aiki tuƙuru da jajircewa ya tafi a banza ba a zamanin jagorancinsa, zai riƙa saka wa masu aiki tukuru.

Zan bar hukumar soji sama da yadda na same ta - Farouk Yahaya

Tun da farko, tsohon COAS da ya sauka, Janar Farouk Yahaya, ya bayyana cewa zai bar hukumar sojin ƙasan Najeriya fiye da yadda ya zo ya sameta a shekarar 2021.

Janar Yahaya ya ce rundunar soji ta samu dumbin nasarori a ƙoƙarin magance matsalar tsaron da ta addabi ƙasar nan karkashin kulawarsa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babban Jigo Ya Tona Asirin Manyan Sarakuna da Wasu Gwamnoni Masu Hannu a Talauta Arzikin Najeriya

Ya roƙi jami'an soji su ci gaba da zama cikin shiri, jajircewa da gwarzantaka yayin sauke nauyin da ke kansu kana su marawa sabon COAS baya domin magance duk wata barazanar tsaro.

Sabon Shugaban 'Yan Sandan Najeriya Ya Sa Labule da Manyan Jami'ai a Abuja

A wani rahoton na daban kuma Sifeta janar da 'yan sandan kasar nan, IGP Egbetokun ya shiga gana wa yanzu haka da manyan jami'an 'yan sanda a Abuja.

Waɗanda aka hanga sun halarci ɗakin taron IG a hedkwatar sun ƙunshi manyan jami'an hukumar 'yan sanda tun daga mataimakan sifetan yan sanda (DIG) da kananan mataimakan sifeta na kasa (AIG).

Asali: Legit.ng

Online view pixel