Mummunan Hatsarin Mota Ya Halaka Mutum 18 a Jihar Kano, Wasu Mutum 12 Sun Jikkata

Mummunan Hatsarin Mota Ya Halaka Mutum 18 a Jihar Kano, Wasu Mutum 12 Sun Jikkata

  • Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan fasinjoji mutum 18 da raunata mutum 12 a jihar Kano
  • Mummunan hatsarin ya auku ne a tsakanin wasu motocin haya guda biyu a garin Zakirai kan hanyar Kano-Ringim
  • Kwamandan shiyya na hukumar FRSC ya gargaɗi direbobi da suka bi a hankali yayin tuƙi da kiyaye dokokin hanya

Jihar Kano - Fasinjoji 18 sun riga mu gidan gaskiya a wani mummunan hatsarin mota a garin Zakirai wanda ke kan hanyar Kano-Ringim, cikin ƙaramar hukumar Gabasawa ta jihar Kano.

Jaridar PM News ta ambato kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, na cewa mutane 12 sun samu raunika yayin da wasu mutum biyar suka tsira ba tare da rauni ba a harin da ya auku ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wasu 'Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Gwamnan Arewa a Hanyar Dawowa Daga Abuja

Mutane 18 sun halaka a wani hatsatin mota a Kano
Wata mota na ci da wuta bayan aukuwar hatsari (Ba a inda lamarin ya auku ba) Hoto: Pmnews.com
Asali: UGC

Wasu daga cikin gawarwakin an binne su tare a wajen da hatsarin ya auku, yayin da sauran aka miƙa su ga ƴan'uwan mamatan.

Kwamandan wanda ƴa tabbatar da aukuwar hatsarin ta hannun kakakin shiyyar, Abdullahi Labaran, ya ce hatsarin wanda ya faru ranar Juma'a da misalin ƙarfe 8:35 na dare ya ritsa ne da motocin haya guda biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ɗora alhakin hatsarin kan matsanancin gudu, tuƙin ganganci da sanya kaya fiye da ƙima wanda hakan ya janyo taho mu gamar motocin inda ɗaya daga ciki ta kama da wuta, rahoton Gazettengr ya tabbatar.

"Hatsarin ya ritsa da fasinjoji 35 a cikin motoci biyu, wanda daga ciki mutum 18 sun ƙone ƙurmus yayin da wasu mutum 12 suka samu raunika." A cewarsa.

Ibrahim ya ƙara da cewa mutanen da suka samu raunika an wuce da su babban asibitin Murtala da ke a birnin Kano.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Wani Almajiri Ya Nutse Cikin Kududdufi a Kano

Kwamandan ya shawarci direbobi da su riƙa tuƙi mai tsafta

Ya shawarci masu motoci da su daina cika gudu, cika lodi da tuƙin ganganci da duk wani abu wanda ka iya janyo aukuwar hatsari a kan hanya.

Kwamandan shiyyar ya kuma koka kan yawan haɗuran da aka samu a jihar Kano cikin satin da ya gabata.

A lokacin da ya kai ziyara inda hatsarin ya auku a ranar Asabar, kwamandan ya jan kunnen masu motoci musamman masu zirga-zirga daga birni zuwa birni da jiha zuwa jiha da su riƙa kiyaye dokokim tuƙi.

Motoci Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota

A wani labarin na daban kuma, wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu motoci a kan titin hanyar Lokoja-Abuja.

Hatsarin ya auku ne tsakanin wata motar haya da motar tankar mai inda nan ta ke gobara ta tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel