“Ina Za Su?” Amarya Da Ango Sun Keta Daji a Kafa, Bidiyonsu Ya Yadu

“Ina Za Su?” Amarya Da Ango Sun Keta Daji a Kafa, Bidiyonsu Ya Yadu

  • Wani ango da amaryarsa sun keta daji da kafa zuwa wajen daurin aurensu kuma bidiyon ya haddasa cece-kuce a TikTok
  • Yan uwa da abokan arziki sun take masu baya yayin da mutumin ya taya amaryar tasa rike rigarta ta baya don kada ya kwashi datti
  • Dan gajeren bidiyon ya haddasa cece-kuce da dama daga masu amfani da TikTok bayan ya yadu a dandalin

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wani ango da amaryarsa suna keta tsakanin daji a ranar daurin aurensu.

Alamu sun nuna sabbin ma'auratan na hanyar zuwa wajen daurin aurensu ne, kuma sun bi ta tsakanin jeji ne.

Ango da amarya a jeji
“Ina Za Su?” Amarya Da Ango Sun Keta Daji a Kafa, Bidiyonsu Ya Yadu Hoto: @user2680246818755.
Asali: TikTok

A bidiyon wanda shafin @user2680246818755 ya wallafa, an gano amaryar a gaba yayin da mijin ke bin ta a baya kut da kut.

Angon ya taya amaryar tasa rike doguwar rigarta ta baya don kada ya nadi datti saboda hanyar na cike ne da ciyayi.

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Rayuwa Babu Ita Ba”: Dan Najeriya Ya Yi Wuff Da Tsohuwar Baturiya, Hotunan Su Yadu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ango da amarya sun taka zuwa wajen aurensu

Wasu yan tsirarun mutane da abokan arziki sun kasance tare da ango da amaryar yayin da suke tafiyarsu gwanin ban sha'awa.

An gano wani mutum da ke tare da ma'auratan dauke da jakar piya wata a kansa.

Yayin da suke tafiya a hanyar, suna ta hira cikin nishadi da harshen garinsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@belilesympa ya yi martani:

"Abubuwa da dama na faruwa a duniyar nan, Mun gode TikTok."

@eliziwangui ya yi martani:

"Za su yawon amarci."

@ashleyk ta yi martani:

"Me yasa sai yau nake ganin auren nan?"

@user3168181197618sarahouattara ya yi martani:

"Amaryar na da sauri sosai."

@Happyangel Nkosi ta ce:

"Ina ta cin karo da bidiyoyin auren nan."

@user2148681097021 ta ce:

"Ina za su?"

Matashi dan Najeriya ya yi wuff da tsohuwar baturiya

Kara karanta wannan

Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka

A wani labari na daban, mun ji cewa wani matashi dan Najeriya daga jihar Delta, Gabriel Aye, ya angwance da masoyiyarsa tsohuwar Baturiya, Kathleen, a jihar Lagas.

An gudanar da shagalin auren ne a kotun Ikoyi inda yan uwa da abokan arziki suka hallara. Ya kuma bayyana cewa ba zai iya rayuwa babu matar tasa wacce ita isa kaka da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel