“Kudi Na Da Karfi”: Dan Najeriya Ya Angwance Da Sahibarsa Baturiya Tsohuwa Tukuf, Hotunan Sun Yadu

“Kudi Na Da Karfi”: Dan Najeriya Ya Angwance Da Sahibarsa Baturiya Tsohuwa Tukuf, Hotunan Sun Yadu

  • Wani dan Najeriya ya yi fice a soshiyal midiya bayan ya angwance da sahibarsa tsohuwar baturiya
  • An tattaro cewa auren da aka yi tsakanin masoyan biyu ya gudana ne a kotun ma'aurata ta tarayya da ke Ikoyi, jihar Lagas
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun garzaya sashin sharhi don taya ma'auratan murna yayin da wasu ke nuni ga tazarar shekarun da ke tsakaninsu

Lagos - Gabriel Aye, wani matashi daga jihar Delta ya angwance da masoyiyarsa tsohuwar Baturiya, Kathleen, a jihar Lagas.

An gudanar da shagalin auren ne a kotun Ikoyi inda yan uwa da abokan arziki suka hallara.

Ango da amarya
“Kudi Na Da Kargi”: Dan Najeriya Ya Angwance Da Sahibarsa Baturiya Tsohuwa Tukuf, Hotunan Sun Yadu Hoto: @gossipmilltv/instagram
Asali: Instagram

Labarin soyayyar ma'auratan ya ja hankali a soshiyal midiya, inda Gabriel ya bayyana cewa ba zai iya rayuwa ba tare da masoyiyar tasa ba.

Aurensu ya haddasa cece-kuce sosai, inda wasu mutane suka jinjinawa soyayyarsu wasu kuma sun soki lamarin.

Kara karanta wannan

Jarumi Kuma Mutum Mafi Tsawo a Najeriya, Afeez Agoro, Ya Rasu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, caccakar bai kawo tangarda ga shagalin bikin ba kuma bai hana shi zama abu mai kyau ba, inda ma'auratan suka dauki rantsuwa da sanyawa junansu zoben alkawari a gaban yan uwa da abokan arziki.

Jama'a sun yi martani

spizy_up ya yi martani:

"Dan uwa mun san cewa fasfot din ne ba za ka iya rayuwa ba tare da shi ba, amma ai muna da kakanni da dama a nan aiii)"

Veevogee ta yi martani:

"Koren fasfot sa'anka ne? Ka auri kakarka saboda dalilai da kai ka fi kowa sani amma yar shekaru 35 a Najeriya ta shirya ita ma. Kuna da ban dariya a duniyar nan fa."

davygrayce ya yi martani:

"Wahala anya ba zan shiga US na auri wata ba. Kaka kamar wannan."

maryann_officiall ya ce:

"Idan da nine nima ba zan iya rayuwa babu ita ba."

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

Matashiyar da aurenta ya mutu cikin watanni bakwai ta yi wa mijinta wankin babban bargo

A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya domin caccakar tsohon mijinta da suka yi zaman aure na watanni bakwai kacal.

Matar ta bayyana cewa mijinta ya muzguna mata a zamansu da juna inda ta ce har kunyar nunawa duniya ita yake yi a matsayin matarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel