Sabon Gwamna Ya Karbe Filayen Gwamnati da Tsohon Gwamna Ya Saidawa Jami’ai

Sabon Gwamna Ya Karbe Filayen Gwamnati da Tsohon Gwamna Ya Saidawa Jami’ai

  • Mohammed Umar Bago ya karbe wasu filayen da gwamnatin Abubakar Sani Bello ta saidawa mutanenta
  • Sanarwar da aka fitar ta ce filayen da sabon Gwamnan ya karbe su na garuruwan Mina, Suleja da Kontagora
  • Gwamnatin Bago tayi umarni a daina daukar sababbin ma’aikata a matakin jiha da duk kananan hukumomi

Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago ya bada umarnin karbe wasu kadarori da dukiyoyin da Abubakar Sani Bello ya saida a ofis.

Daily Trust ta ce an soke saida kayan gwamnatin Neja da aka yi wa kwamishonni, jami’an gwamnati da daidaikun mutane a gwamnatin baya.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar gidaje da filaye, Abdul Husaini, ya fitar da sanarwa cewa an karbe filayen gwamnati da saida a fadin jihar.

Gwamna
Sabon Gwamnan Neja, Umar Bago wajen taro da CECC Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Wasu filaye aka karbe?

Abdul Husaini ya ce wuraren da abin ya shafa sun hada da filin hukumar kula da datsen ruwa a Sabon Wuse; yankin Three Arms Zone da ke Minna.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC A Babbar Jihar Arewa Ya Kori Kwamishina Da Wasu Mukarrabansa Guda 2

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika gwamnatin Mohammed Umar Bago ta karbe filayen titin hanyar bayan gari da kuma na ma’aikatar kula da jeji da suke garin Kontagora.

Sannan an karbe filin da aka mallakawa Maximum Shelter a Suleja da filin da tsohon Gwamna ya ba kamfanin Abuja Steel Extension a garin Dikko.

Kamar yadda rahoto ya zo a baya, gwamnatin jihar Neja ta karbe lasisin mallaka na CofO da aka ba jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida a Suleja.

Sanarwar ta ce karbe filin ya shafi wani gidan mai da aka amince a gina Keteren Gwari.

Daukar aiki da aka yi

Jaridar ta ce Mohammed Umar Bago ya bada umarnin a soke duk wasu aiki da wanda ya gabace shi, Abubakar Bello ya dauka kafin ya bar mulki.

Gwamnatin Bello ta dauki sababbin ma’aikata a daidai lokacin da ake shirin canza gwamna. A yanzu an tsaida daukar aiki a jiha da kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Ci Gaba Da Aikin Rusau Bayan Zazzafan Musayar Yawu Da Aka Yi Tsakanin Ganduje Da Kwankwaso

Shugaban ma’aikatan gwamnatin Neja, Abubakar Y. Salisu ya fitar da takarda ya na mai bada sanarwa cewa gwamna Bago ya bada wannan umarni.

Rushe-rushe a jihar Kano

Cikin daren yau kwatsam aka ji labarin rusa shatale-talen ke kan titin shiga gidan Gwamnatin Kano. Wannan ya jawo suka daga gida da wajen jihar.

Barista Abba Hikima wanda ya na goyon bayan gwamnatin, ya soki rusa shatele-talen. Daga baya gwamnatin Jihar ta bayyana dalilin yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel