Bashir Ahmed: Tsohon Hadimin Buhari Ya Fito A Bidiyon Barkwanci

Bashir Ahmed: Tsohon Hadimin Buhari Ya Fito A Bidiyon Barkwanci

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed, ya fara bayyana a bidiyon barkwanci
  • An dai gano Bashir a cikin wani dan gajeren bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya inda ya bayyana a matsayin jami'in DSS
  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyon tsohon hadimin Buharin wanda ke kasar China inda ya je yin kwas

Yan makonni bayan sauka daga karagar mulki, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed ya koma yin bidiyon barkwanci.

A bidiyon wanda abokin wasan barkwancin nasa mai suna @BelloGaladanchi ya wallafa a Twitter, Bashir ya fito ne a matsayin jami'in hukumar tsaro na farin kaya wato DSS.

Bashir Ahmed da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
Bashir Ahmed: Tsohon Hadimin Buhari Ya Fito A Bidiyon Barkwanci Hoto: Pulse Nigeria
Asali: UGC

An jiyo Bello Galadanchi wanda aka fi sani da Dan Bello yana kokawa cewa ya shiga hannun tsohon hadimin shugaban kasar inda shi kuma Bashir ya ce daga nan sai DSS zai kai shi.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Dama dai Bashir din ya tafi yin kwas a China inda shi kuma Galandanci a chan kasar yake aikin koyarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli bidiyon nasu a kasa:

Martanin jama'a a kan bidiyon

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kan bidiyon a kasa:

@queenfareejarma ta yi martani:

"@BashirAhmaad na ji dadin saukin kai irin naka da har ka yarda ka yi wasa da Kawu Mansur @BelloGaladanchi domin nishadantar da mu. Kana bukatar lokaci bayan duk wahalar da ka sha. Nagode kuma ka ci gaba da yin abun da ke sanya ka farin ciki "

@Nawas_masood ya ce:

"Kasa da makonni biyu da karewar gwamnatin Buhari Bashir har ya fara wasan barkwanci, a'a a'a wannan bai yi dadi ba ."

@isasquare ya ce:

"Haha... Wannan akwai ban dariya. Ban san cewa @BashirAhmaad na kunyar kamara ba."

@Kaveer_gaya ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

"Daga barin Gwmnati sai mutum ya fara comedy, ko ba'a biya fansho bane."

@____Auwal ya ce:

"Ban taba tunanin @BashirAhmaad zai karbi wannan ba, gaskiya saukin kansa ya burge ni."

@Moh_mahuta_ ya ce:

"Su @BashirAhmaad fa an koma bidiyoyin barkwanci ."

@BashirZubayr ya ce:

"Wato @BashirAhmaad Mulki ya qare ka koma comedy."

Matashiya ta fallasa irin son da take yi wa mijinta mai nakasa

A wani labari na daban, wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna sauyawar wani matashi wanda ke da lalura ta shan inna.

Jemimah wacce ta ce kyakkyawan mutumin mijinta ne ita ce ta wallafa bidiyon a kan manhajar TikTok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel