“Yana Da Kyau”: Bidiyon Sauyawar Wani Mai Lalurar Nakasa Bayan Shekaru 10 Ya Dauka Hankali

“Yana Da Kyau”: Bidiyon Sauyawar Wani Mai Lalurar Nakasa Bayan Shekaru 10 Ya Dauka Hankali

  • Hotunan sauyawar wani matashi mai lalurar shan inna wanda ya gaji da haduwa don kyau ya yadu kuma ya haddasa cece-kuce a TikTok
  • Wata mai amfani da TikTok, Jemimah ta wallafa hotunan a wani bidiyo tana mai sanar da mutane irin so da kaunar da take yi wa mutumin
  • A wani tsohon hoto da aka dauka shekaru 10 da suka gabata, an gano mutumin yana dan karamin yaro, amma hotunan shi na yanzu ya nuna sauyawarsa gaba daya

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuna sauyawar wani matashi wanda ke da lalura ta shan inna.

Jemimah wacce ta ce kyakkyawan mutumin mijinta ne ita ce ta wallafa bidiyon a kan manhajar TikTok.

Matashi mai lalurar nakasa
“Yana Da Kyau”: Bidiyon Sauyawar Wani Mai Lalurar Nakasa Bayan Shekaru 10 Ya Dauka Hankali Hoto: TikTok/@e_jemimah
Asali: TikTok

Mutumin na da lalurar shan inna a kafafunsa biyu wanda hakan ya sa suka shanye sai dai kuma hakan bai raba shi da kyawun fuskar da Allah ya yi masa ba.

Kara karanta wannan

"Ta Kwashe 'Ya'yana Ta Tafi Da Su": Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Da Suka Dade Ta Rabu Da Shi

Hotunan sauyawar wani matashi cikin shekaru 10 ya haddasa cece kuce

Manufar bidiyon wanda ke dauke da hotuna da dama a ciki shine don nuna yadda mutumin ya sauya gaba daya cikin shekaru 10.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An dauki mutumin a hoton farko da ya bayyana a bidiyon lokacin yana makaranta. Yana sanye da kayan makarantarsa.

Wani hoton kuma ya nuno sa lokacin da ya kammala makarantar jami'a, sannan ya yi hoton ne da abokan karatunsa.

Baya ga tsoffin hotunan, sabbin hotunan da aka gano a bidiyon ya nuna sauyawar mutumin gaba daya wanda a yanzu ya kara haske da gogewa.

Jemmimah ta fallasa son da take yi wa mutumin. Ta rubuta a jikin bidiyon:

"Ina kaunarsa da dukkan zuciyata."

Ba a tabbatar da ko da gaske mutumin mijin Jamimah bane domin wasu mutane sun ce kaninta ne.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@user4218371324079 ya ce:

"Kin tabbata cewa kina son sa, ko dai saboda kudi ne?"

Bibi_couture_kids:

"Abu mai dadi daya game da dan adam ko kai wanene, a duk yadda kake, akwai wani mutum da zai so ga ba tare da dalili ba sannan su zamo abokanka."

@Blissokeke ta yi martani:

"Wannan dan uwanki ne hajiya."

@nyeneimeekanem206 ta ce:

"Yana da kyau sosai."

Matashiyar da aurenta ya mutu cikin watanni bakwai ta yi wa mijinta wankin babban bargo

Wata matashiya yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya domin caccakar tsohon mijinta da suka yi zaman aure na watanni bakwai kacal.

Matar ta bayyana cewa mijinta ya muzguna mata a zamansu da juna inda ta ce har kunyar nunawa duniya ita yake yi a matsayin matarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel