Bidiyo: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Emefiele Yayin da Ya Shiga Jirgin Sama

Bidiyo: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Emefiele Yayin da Ya Shiga Jirgin Sama

  • A ranar Asabar, 10 ga watan Yuni ne rundunar tsaro ta farin kaya wato DSS ta tabbatar da tsare gwamnan babban bankin CBN da aka dakatar
  • Wani bidiyo ya bayyana a soshiyal midiya inda aka gano jami'an tsaro kewaye da Godwin Emefiele yayin da ya shiga cikin jirgin sama
  • A daren ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni ne shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan na CBN daga kujerarsa domin gudanar da bincike a kansa

Wani bidiyon jami'an tsaro kewaye da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a wani filin jirgin sama da ba a san ko ina ne ba ya bayyana a soshiyal midiya.

A bidiyon wanda jaridar Daily Trust ta wallafa a shafinta na Twitter, an gano dakataccen gwamnan na CBN mafi dadewa a tarihin kasar sanye da riga da wando na yadi da kuma hula da ya dace da kayan.

Godwin Emefiele
Bidiyo: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Emefiele Yayin da Ya Shiga Jirgin Sama Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jami'an tsaro sun marawa Emefiele baya zuwa cikin jirgin sama

Wata mota kirar Toyota Hilux ta faka a hankali a gaban wani jirgin sama yayin da jami'an tsaro sanye da kayan gida suka bude masa kofa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daya daga cikin jami'an tsaron wanda ke rike da ankwa a hannunsa na dama ya rufa ma Emefiele baya zuwa cikin jirgin saman, yayin da sauran suka biyo bayansu.

Sai dai kuma ba a tabbatar da lokacin da aka nadi bidiyon ba amma dai wasu masu amfani da soshiyal midiya sun ce an dauke shi a lokacin da aka kama tsohon gwamnan na CBN.

Legit.ng ba za ta iya tabbatar da bidiyon kai tsaye ba. Kalle shi a kasa:

Godwin Emefiele: Gwamnan CBN da aka dakatar yana hannunmu, DSS

A wani labarin, mun kawo a baya cewa dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, na tsare a hannun jami’an tsaro na farin kaya (DSS.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, Peter Afunanya ya fitar a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni.

Hakan na zuwa ne yan awanni bayan DSS ta karyata rade-radin cewa Emefiele yana tsare a hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel