Yanzu Yanzu: Dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Baya a Hannunmu, In Ji DSS

Yanzu Yanzu: Dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Baya a Hannunmu, In Ji DSS

  • Hukumar DSS ta yi martani a kan rahotannin da ke yawo cewa ta kama dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele
  • Rundunar yan sandan farin kaya ta ce a yanzu haka Emefiele wanda aka dakatar a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni baya tsare a hannunta
  • Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya dakatar da gwamnan na CBN har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan ofishinsa

Abuja - Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta ce dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, baya tsare a hannunsu, jaridar The Cable ta rahoto.

Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele a ranar 9 ga watan Yuni, ya kuma bada umurnin a cigaba da bincike kan abubuwan da ya aikata lokacin yana gwamnan babban bankin na Najeriya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Biyo bayan dakatar da Emefiele a ranar Juma'a, wasu rahotanni sun bayyana na cewar jami'an DSS din sun kama shi.

Jami'in DSS da Godwin Emefiele
Yanzu Yanzu: Dakataccen Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Baya a Hannunmu, Inji DSS Hoto: Department of State Services (DSS) and CBN
Asali: Facebook

A yanzu haka Emefiele baya tsare da mu, DSS

Sai dai kuma, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter a safiyar Asabar, 10 ga watan Yuni, hukumar DSS ta ce sam dakataccen gwamnan CBN din baya tsare a hannunta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta rubuta a shafin nata:

"Yanzu haka, Emefiele baya tare da DSS."

Wike ya yaba ma Tinubu kan dakatar da Emefiele daga matsayin gwamnan CBN

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jinjinawa shugaban kasa Bola Tinubu kan dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Da yake martani ga ci gaban, Wike, daya daga cikin mutanen da suka soki manufofin Emefiele, musamman sauya fasalin naira, ya bayyana matakin da shugaban kasar ya dauka a matsayin wanda ya dace kuma kan lokaci.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Ya ce wannan na nuna lallai Tinubu yana da alkibla da kokarin tabbatar da kawo ci gaba a kasar Najeriya kamar yadda ake muradi.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma yaba ma shugaban kasa Tinubu kan amincewa da shekarun ritaya da fansho na ma'aikatan shari'a a kasar, a cewar wata sanarwa da tawagar labaransa suka fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel