Mutane Da Dama Sun Tsere Yayin da Yan Bindiga Suka Kashe Manoma 50, Sun Sace Shanu a Neja

Mutane Da Dama Sun Tsere Yayin da Yan Bindiga Suka Kashe Manoma 50, Sun Sace Shanu a Neja

  • Tsagerun yan bindiga sun dawo da kai hare-hare a wasu garuruwan jihar Neja da ke arewa maso tsakiya
  • Yan bindiga da yawansu ya fi 100 sun yi wa kauyukan tsinke tun daga ranar Juma'a har zuwa wayewar garin Asabar
  • Kimanin mutane 50 ne suka kwanta dama a hare-haren da ya gudana a karamar hukumar Rafi

Niger - Rahotanni sun kawo cewa mutane da dama sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka halaka akalla mutum 50 a wani farmaki da suka kai garuruwa daban-daban a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun kai hare-haren ne tsakanin ranar Laraba da Asabar.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Mutane Da Dama Sun Tsere Yayin da Yan Bindiga Suka Kashe Manoma 50, Sun Sace Shanu a Neja Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A harin baya-bayan nan da suka kai kan kauyuka biyar wanda ya gudana tsakanin karfe 2:00pm na ranar Juma'a da safiyar Asabar, an rasa rayuka da ba a san adadinsu ba yayin da aka sace wasu da dama ciki harda mata da yan mata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Rai, Sun Yi Garkuwa da Sarakuna 2 a Jihar Bauchi

An tattaro cewa yayin da mutane 13 suka rasa rayukansu a garin Kusherki, an kashe mutum 12 a kauyen Gidigori sannan har yanzu ba a kai ga tantance wasu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa lamura sun kara cakudewa a yankin tun a ranar Laraba yayin da daruruwan mutane suka rasa muhallinsu.

An tattaro cewa mutane da dama da suka hada da mata da yara sun yi tururuwan fita daga kauyukan zuwa Kagara, hedkwatar karamar hukumar Rafi, inda suka barwa yan bindiga kauyukansu inda suka koma kwana a gidajensu.

Daya daga cikin manoman da suka tsere, Abdullahi Usman ya bayyana cewa yan bindigar da yawansu ya fi 100 sun shigo kan kimanin babura 50, sannan suka kwace kauyuka da dama tun daga misalin karfe 2:00pm na ranar Juma'a sannan sun yi aiki har zuwa safiyar Asabar ba tare da tangarda ba.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Sanatan APC ya sharbi kuka a majalisa, ya fadi sharrin da aka masa

Usman ya ce:

"Da gaske ne cewa yan bindiga sun dawo da hare-hare cike da karfi. Ba mu ji ta dadi ba cikin makonni biyu da suka gabata amma lamarin ya kara muni ne tun Laraba.
"Yanzu haka da nake magana da ke, yan bindiga sun kwace yawancin yankunan karamar hukumar Rafi. Suna a garin Kusherki tun da misalin karfe 2:pm a ranar Juma'a; sun kashe dare a Garin-Zara sannan suka sace daruruwan dabbobi da kuma kashe wasu mutane da ba a san yawansu ba."

Mutanen da abun ya ritsa da su sun yi zargin cewa sojojin da ke Kagara da Pandogari basu maida martani ga hare-haren ba, cewa kawai dai suna sintiri ne a garin Kagara.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigar sun raba kansu gida biyu inda daya suka farmaki garin Sakaba, kasa da kilomita 4 daga garin Kagara, sannan daya bangaren sun shiga garin Tungan-Makeri, kilomita 15 ga Kagara inda suka sace dabbobi da mutum biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Ina da tabbacin Tinubu da Bago za su magance lamarin, Sanata Sani Musa

Sanata mai wakiltan yankin Neja ta gabas a majalisar dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa ya koka cewa yan bindigar sun dawo da kai hare-hare kan kananan hukumomin Rafi, Paikoro, Munya da Shiroro duk a mazabarsa.

Ya ce miyagun sun fito don gwada iko da karfin sabbin gwamnatoci a matakan jiha da tarayya.

Sai dai kuma, ya yarda cewa gwamnatocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Mohammed Umar Bago za su magance lamarin.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an tura jami'an tsaro zuwa yankin don magance lamarin.

Abiodun ya ce:

“Mun yi nazari a kan dabarun da aka tura yankin, kuma an tura karin jami’an yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji don yin aiki a garuruwan Yakila, Tegina, Kagara, Pandogari, Kusherki da kewaye domin hana sake aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Rusau: Dubu ta Cika, 'Yan Sanda Sun Sake Kwamushe Mutane 57 Bisa Zargin Dibar Ganima

"Rundunar hadin gwiwa suna aiki tukuru don ganin an ceto wadanda aka sace ba tare da wani rauni ba."

Legit.ng ta zanta da wani dan asalin yankin Rafi mazaunin garin Minna mai suna Sani Suleiman inda ya tabbatar da lamarin.

Suleiman ya ce:

"Al'ummarmu sun ga tashin hankali ba kadan ba. Yanzu haka akwai wasu daga cikin danginmu da suka zo neman mafaka a nan gidana saboda suna tsoron abun da zai kara biyo baya a nan gaba.
"Muna farin ciki cewa abubuwa sun lafa sai ga shi maharan sun dawo da karfinsu. Muna kira ga sabbin gwamnatoci da su kawo mana dauki domin ko da ba a gida nake zaune ba hankali ba zai kwanta ba muddin yan uwana suna cikin mawuyacin hali."

Sojoji sun yi luguden wuta kan yan Boko Haram a jihar Borno

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar Jama'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wal-Jihad (JAS) ta Boko Haram, ta ƙara shan kashi a hannun dakarun sojin saman Najeriya a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Jiragen yaƙin dakarun sojin saman sun yi luguden wuta a maɓoƴar ƴan ta'addan da ke a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel