Sabon Yayi: Kotu Ta Tasa Keyar Dan Damfara Zuwa Ofishin EFCC Don Karbar Lakca, Ta Gindaya Masa Ka'idoji

Sabon Yayi: Kotu Ta Tasa Keyar Dan Damfara Zuwa Ofishin EFCC Don Karbar Lakca, Ta Gindaya Masa Ka'idoji

  • Kotun da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta tura wani dan damfara zuwa ofishin EFCC don karbar lakca
  • Alkalin kotun, Aliyu Shafa ya umarci matashin da ya rinka zuwa ofishin da safe har zuwa karfe 12 na rana kullum
  • Hukuncin ya kunshi koya wa matashin sanin amfani da kuma rashin amfanin damfara a rayuwarsa ta yau da kullum

FCT, Abuja - Kotu ta tura wani matashi mai suna Ndubisi Success zuwa ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) don masa lakca na mako guda.

Kotun da ke zamanta a Gwagwalada cikin birnin Tarayya Abuja ta umarci a kai shi ofishin hukumar ne don a koya masa sanin amfanin damfara da kuma rashin amfanita, cewar Legit.ng.

Kotu ta tura matashi ofishin EFCC don karbar lakca
Kotu Ta Tasa Keyar Dan Damfara Zuwa Ofishin EFCC. Hoto: EFCC.
Asali: Facebook

Alkalin kotun, Aliyu Shafa ya umarci wanda ake zargin da ya bi umarnin kotun don ya karu.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

Alkalin kotun ya saka masa ka'idojin da zai bi a yayin da yake zuwa ofishin hukumar

An umarci wanda ake zargin ya ziyarci ofishin hukumar da misalin karfe 9 na safe zuwa karfe 2 na rana har na tsawon mako guda don samun ilimi akan illolin damfara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar tana zargin Ndubisi da kirkirar shafin Instagram na bogi Don damfarar mutanen ba su ji ba, ba su gani ba.

Har ila yau, wanda ake zargin zai kasance karkashin kulawar daraktan kula da harkar shari'a ta hukumar, cewar rahotanni.

Mai Shari'a Shafa yayin yanke hukuncin ya ce:

"Na saurari roko daga wanda ake zargi da kuma lauyan masu kara cikin natsuwa.
"Yawan damfara a cikin al'ummar mu ta yi yawa, damfara ta yanar gizo ta na da hatsari kuma dole mu kawo karshenta."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka Bayan Janye Tallafin Fetur

Lauyan hukumar ya bukaci a mallakarwa Gwamnatin Tarayya wayar dan damfarar

Lauyan hukumar, Chidike Obasi-Oko ya fada wa kotu cewa a shekarar 2022, Ndubisi ya yi yunkurin damfarar mutane ta hanyar amfani da shafin Instagram na bogi don a tura masa kaya ko kudi.

Ya ce hakan ya sabawa dokar kasa inda ya bukaci wayar REDMI da yake amfani da ita a kwace ta don mallakarwa Gwamnatin Tarayya.

Rashin Daraja: DJ Ya Addabi 'Yan Islamiyya da Kida Ya Gamu da Fushin Alkali

A wani labarin, kotun da ke zamanta a jihar Kano ta tsare wani matashi mai kayan kida saboda damun makarantar Islamiyya.

Kotun ta tuhume shi ne saboda ya na hana daliban makarantar sauraron abin da malamansu suke koya musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel