Bamu Yarda Akwai Wani Tallafin Man Fetur Ba a Najeriya, ASUU

Bamu Yarda Akwai Wani Tallafin Man Fetur Ba a Najeriya, ASUU

  • Kungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta bayyana matsayarta kan batun tallafin man fetur da ake ta kace-nace
  • Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce tuntuni ba su yarda akwai wani abu mai sun tallafin mai ba a Najeriya
  • Ya ce FG ta kashe biliyoyin kuɗi a kokarin gyara matatun mai na gida amma har yanzu suna nan a mace

Ebonyi - Shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i a Najeriya (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce ko kaɗan ƙungiyar ba ta yarda akwai tallafin man Fetur ba a ƙasar nan.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar a wurin bikin rantsarwa cewa, "Tallafin mai ya tafi,"kuma hakan ya jawo tashin farashin litar mai da ƙuma ƙaranci a faɗin Najeriya.

Farfesa Emmanuel Osodeke.
Bamu Yarda Akwai Wani Tallafin Man Fetur Ba a Najeriya, ASUU Hoto: Emmanuel Osodeke
Asali: UGC

Da yake jawabi a wurin wata lakca a jami'ar Alex Ekweme da ke Ndufu-Alike, a Ikwo, jihar Ebonyi, shugaban ASUU ya ce yana mamakin yadda Najeriya ke haƙo ɗanyen mai amma ba zata iya tace shi a gida ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Da Atiku Ba Su Cancanci a Ayyana Su Matsayin Shugaban Kasa Ba, Shaidar Atiku Ya Fadawa Kotu

Channels tv ta rahoto Farfesa Osodeke na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A zahirin gaskiya bamu amince akwai tallafin man fetur ba, ba zai yuwu a ce kana haƙo ɗanyen mai tsawon shekaru 70 da suka wuce amma ba zaka iya tace shi a gida ka sayar wa mutane a farashin kuɗin Najeriya ba. Akwai wata a ƙasa."

A wurin lakcar mai taken, "Faɗaɗa ilimin fasaha ta hanyar nagartaccen ilimi a mahangar ASUU," shugaban ƙungiyar ya koka kan yadda Najeriya ta gaza kafa matatar mai ɗaya tal mai rai.

Haka nan ya koka kan yadda gwamnati ke cewa ta kashe makudan kuɗaɗe kan matatun mai da ake da su a ƙasar nan, amma basu taɓuka aikin komai.

"Najeriya ta kashe biliyoyin naira cikin shekaru uku da suka gabata ko fiye da haka wajen kokarin tashin matatun da muke da su amma har yanzu a mace suke. A yanzu kananun ƙasashe suna da matatu masu rai."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule Da Kungiyar Ma'aikata Ta Kasa Kan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

A Karon Farko, Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Gwamnonin Jihohi a Abuja

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga taro da kafatanin gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan a Aso Rock.

Wannan zama shi ne karo na farko da shugaba Tinubu ya yi da kafatanin gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 tun bayan da ya karɓi rantsuwar kama aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel